Home Ilimi Rinton Makin Jamb: Mmesoma Ta Tuba A Gaban Majalisar Wakilai

Rinton Makin Jamb: Mmesoma Ta Tuba A Gaban Majalisar Wakilai

201
0
20230719 161834

A kokarin  ta na tabbatar da gaskiyar ko Mmesoma Joy Ejikema yarinyarnan yar asalin Jihar Anambra da ta kara makin jarabawar ta ko a ‘ a Majalisar ta tabbatar da laifin yarinyar.

” yarinyar ta karbi laifinta a gaban kwamitin Majalisar Wakilai jiya Laraba ”

Mmesoma ta baiyana a gaban kwatin tare da iyayenta da su kansu Hukumar ta Jamb.
Ba tare da bata lokaci ba Mmesoma ta tabbatar wa da kwamitin cewa gaskiya ne inta ta kara makin da ga 249 zuwa 360 amma ta na neman afuwar Hukumar Jamb da Majalisa da ma Yan Najeriya baki daya.
20230719 163051
Hon. Abubakar Fulata, Dan Majalisar Wakilai mai Wakiltar kananan hukumomin Birniwa/Kiri kasamma/Guri da ga Jihar Jigawa na daga cikin Yan kwamitin da suka binciki Mmesoma yace yarinyar ba ta wahalshe da su ba ta amsa laifinta.
Ya ce binciken su ya tabbatar da gaskiyar batum cewa waye ya ke da gaskiya Hukumar Jamb ko Mmesoma? ” yanzu kowa ya san waye mai gaskiya, shine burin binciken kwamitin mu” inji Hon. Fulata.
Hukumar Jamb ta tabbatar wa da kwamitin cewa hukumar ta na da kariya mai karfi akan shafin Yanar Gizo nata yana da wahala ayi mata kutse.
Daraktan Hukumar ya ce Yarinyar ta yi kokarin ta saka gyaran da ta yi cikin shafin na su amma matakan kariya su ka hana ta.
Kwamitin Majalisar Wakilai ya ce ba su da masaniya na hukunci da za a yankewa Mmesoma da sauran wadan da aka kama da laifin kara makin sai dai kotu.
20230719 172942
Fulata ya ce za su rubuta rahoton su su gabatar a gaban Majalisa kamar yadda tsarin ya ke.
Sai dai ya ja hankalin Mmesoma da sauran masu hali irin nata da su guji aikata hali irin nata; inda ya kara da cewa makin da ta samu zai bata gurbi a duk jami’oin Najeriya ba sai ta kara maki ba.
Hukumar Jamb ta ma ka Mmesoma a kotu kuma tuni ta dakatar da ita da ga sake rubuta jarabawa sai bayan shekaru uku bayan ta soke jarabawar da ta yi.
Ko tuban da Mmesoma  ta yi a gaban Majalisar zai sa kotu ta yi mata rangwame ko a’a , lokaci  ne kawai zai tabbatar da  hakan.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here