Home Addini Yadda Musulmi Miliyan 1.5 Suka Gudanar Da Ibada Ranar Arfa

Yadda Musulmi Miliyan 1.5 Suka Gudanar Da Ibada Ranar Arfa

2
0
Arafat

Musulmai fiye da miliyan 1.5 ne ke gudanar da aikin Hajji a Saudiyya.

Aikin Hajji ɗaya ne daga cikin ginshiƙan addinin Musulunci, wanda ake son kowane Musulmi ya yi idan ya samu hali.

 

A Yau Talata, 26 ga watan Mayun 2026 ne ake gudanar da hawan Arfa na aikin Hajjin shekarar 1447 bayan Hijira.

 

 

A cewar malamai, ranar Arfa ce mafi falala a cikin ranaku.

Sheikh Isa Ali Pantami ya ce ranar Arfa ita rana mafi daraja cikin ranakun shekara da Allah ya hallita.

 

”Kamar yadda a cikin darare babu daren da ya kai na laylatul qadar falala, haka ma a cikin ranaku babu wadda ta kai ranar Arfa falala da daraja a wajen Allah”, in ji Sheikh Pantami.

 

Sheikh Pantami ya ce saboda daraja da falalar ranar Allah S.W.T da kansa ya ambaci sunan ranar a cikin Alqur’ani mai girma, cikin suratul Bakara aya ta 198.

 

Shehin malamin ya ce a ranar ce kuma Allah ya cika wa bayinsa addininsa.

 

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here