Home Siyasa Majalisar Wakilan Najeriya Ta Umarci NERC Da Ta Dakatar Da Yunkurin Karin...

Majalisar Wakilan Najeriya Ta Umarci NERC Da Ta Dakatar Da Yunkurin Karin Kudin Wuta A Kasar

147
0
Reps Plenery

A yunkurinta na ganin ba a sake jefa Yan Najeriya cikin Karin matsin tattalin arziki ba, Majalisar Wakilan Najeriya ta bukaci hukumar kula da wutar lantarki ta kasa NERC da kada ta kuskura ta amince da yunkurin karin kudin wutar lantarki  da akeyi a Najeriya.

Majalisar ta dauki wannan matakin ce biyo bayan wani kudiri da Hon Aliyu Madaki daga Jihar Kano ya gabatar da ya bukaci dakatar da Shirin Karin a zaman Majalisar na ranar Alhamis.

Da yake jagorantar muhawarar, Hon Madaki, ya bayyana cewa, a baya-bayan nan, Kamfanonin rarraba wutar lantarki (DISCOS) sun sanar da abokan huldarsu wani shiri na karin kudin wutar lantarki.

Dan Majalisar ya ce a karkashin shirin na Karin kudin wutar lantarki da aka kudiri aniyar yi, kwastomomin da ke dauke da mitoci na rukunin ‘B’ da ’ C’ masu samun wutar lantarki ta tsawon sa’o’i 12 zuwa 16 a kowace rana za su biya Naira 100 kan kowace KWh, yayin da Rukunin ‘A’ da ke samun wutar awoyi 20 zuwa sama da kuma’ runkinin B’ za su sami Karin kudi mai yawa.
Ya kara da cewa wadanda basu da mita kuma, za su sami gagarumin Kari.

20230720 164612

Har ila yau, ya bayyana cewa, sanarwar da gamayyar kanfanonin rarraba wutar lantarki DISCOS ta fitar ta bayyana cewa, daga ranar 1 ga Yuli, 2023, za a Kara kudin da masu amfani da wutar lantarkin suke biya.

Alhaji Madaki ya nuna damuwarsa kan yadda ake shirin karin kudin wutar lantarkin duk da gazawar kamfafonin wajen samar da akalla megawatt 5,000 a duk shekara bayan sanya hannu kan kwangila da hukumar NERC.

Ya Kara da cewa bai dace ba Kuma rashin tausayi ne a bullo da batun karin farashin wutar lantarkin a wannan lokaci da ‘yan Najeriya da dama suke fama da radadi sakamakon karin farashin man fetur.

Ya kara da cewa karin kudin da ake shirin yi bai dace da bukatun talakawan Najeriya ba, haka kuma ba don amfanin al’ummar kasa ba ne, sannan karin kudin da ake shirin yi na cin karensu babu babbaka ne.

Da yake bayar da gudunmuwa a muhawarar wani Dan Majalisa daga jihar Legas Mista Babajimi Benson, ya bayar da hujjar cewa ya kamata a gayyaci kanfanonin DISCOS da GENCOS don jin ta bakinsu saboda tashin farashin kayayyaki da kuma karuwar farashin canjin kudin kasashen wajen.

Shi kuwa Bamidele Salaam daga jihar Osun, ce ya yi ya kamata gwamnati ta inganta jin dadin ma’aikata domin su samu damar iya biyan kudin maimakon dakatar da shi.

Da take amince da kudirin, majalisar ta umurci kwamitin kula da wutar lantarki (idan an kafa shi) da ya tattauna da hukumar Samar da wutar lantarki ta Kasa NERC domin samun matsaya daya wajen tinkarar wannan yunkuri da ake shirin yi na kara kudin amfani da wutar lantarki

 

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here