Home Cinikaiyar Zamani Najeriya Za Ta Fara Karbar Haraji Ga Miliyoyin ‘Yan Kasuwar Kasar

Najeriya Za Ta Fara Karbar Haraji Ga Miliyoyin ‘Yan Kasuwar Kasar

249
0
Traders 1

Hukumar tara kudaden shiga ta Najeriya ta fada a ranar Litinin din da ta gabata cewa ta hada gwiwa da kungiyar ‘yan kasuwa domin karbar harajin kayayyaki na (VAT) daga miliyoyin kananan ‘yan kasuwar, wani bangare na yunkurin fadada kudaden shiga da gwamnatin shugaba Bola Tinubu ke yi.

Najeriya na daya daga cikin kasashe mafi karancin tattara kudaden haraji a duniya da kusan kashi 10.8% na GDP, a cewar hukumar tattara haraji ta kasa FIRS.

Kashi 47% kacal na kasafin kudin bana zai fito ne daga kudaden shiga, sauran kuma daga rance.

Hukumar ta FIRS ta fada a cikin wata sanarwa da ta fitar cewa tana hada hannu da kungiyar ‘yan kasuwar Najeriya (MATAN) domin karba da kuma fitar da kudin harajin VAT daga mambobinta, musamman ma wadanda ba na yau da kullun ba, ta hanyar amfani da na’urar zamani.

Ta ce hadin gwiwar za ta taimaka wajen “dakatar da ayyukan masu karbar haraji ba bisa ka’ida ba a kasuwannin Najeriya.”

Kungiyar ta MATAN ta ce tana da ‘yan kasuwa sama da miliyan 40, galibi a bangaren da ba na yau da kullun ba, inda akasarin ‘yan Najeriya ke samun kudin shiga.

Hukumar tattara kudaden shigar ta ce mambobin kungiyar ta MATAN za su karbi katin shaida tare da lambobin tantance haraji sannan kuma na’urar zamani za ta bi diddigin kudaden da suka karba don biyan haraji.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here