Home Game da Mu

Game da Mu

Game da Viewfinder

TARIHI

An fara buga Jaridar Viewfinder (ISSN: 2141-3843), bugun takarda a watan Juni na shekara ta 2011. Kamfanin Allyman Media & Publishing Limited (RC: 628436) ne, wanda Hukumar da take Yiwa Kamfanoni Rijista wato CAC ta yiwa wannan kamfani Rejista a watanYuli na Shekara ta 2005.

Shekaru biyu da rabi da Kamfanin ya shafe yana buga wannan jaridar ba tare da tsaiko ba; shekaru ne masu cike da da rusu da kalu- bale. Babban Kalu-balen da Kamfanin ya fuskanta shine rashin wadatattun kudade na gudanarwa; sakamakon rashin hadinkai  da rashin goyon baya daga gwabnatti da kuma wasu masu bada tallace-tallace.

Duk da irin wadannan kalu-bale da jaridar ta fuskanta; tayi rawar gani domin kuwa ta taka muhimmiyar rawa wajen zakulo labarai masu mahimmanci wadanda suka ja hankalin gwabnati tare da fadakar da al’umma akansu.

Kuma jaridar ta samu damar gudanar da aiyukanta a jahohi goma sha uku dake Arewacin Kasarnan inda suke aiko da rahotanni.Ko da yake an fuskanci kalu-bale daga gwabnatoci sakamakon fede gaskiya da nusar da gwabnati akan hakkin daya rataya a wuyanta.

Chanjin gwamnati da akayi a shekara ta 2013, ya kawo chanjin dokoki na gudanarwa; wanda hakan yasa jaridar bata samun tallace-tallace kamar yadda ya kamata ba; hakan ya shafi shigowar kudaden shiga. Abun daya tilasta  aka dakatar da buga jaridar a shekara ta 2014.

Bayan hutun dole na tsawon shekaru takwas da jaridar tayi; mun sake bijiro muku da wannan Jarida wato viewfinderng.com wacce za’a rinka bugawa a yanar GIZO –GIZO, wato online.

Kuma zata rinka zakulo labarai ne daga kwararrun marubutanmu akan muhimman batutuwa a fannoni da  dama kamarsu: Harkar Noma da Kiwo  da Lafia da Ilimi da batum Yanayi da Siyasa da Sadarwa ta Zamani da  Cinikaiya ta Zamani, da Nishadantarwa da Labarun Wasanni da kuma Labaru masu ratsa Zuciya da sauransu.

Jaridar viewfinderng.com, zata cigaba da kasancewa karkashin Kamfanin Allyman Media & Publishing Limited wanda yake gudanar da aiyukansa a fannoni da dama musamman wadanda suka shafi harkarJarida.

HANGEN MU

Hangen mu shine, mu kasance daga cikin Kamfanoni wadanda suke da burin zama fitattu, masu fadaaji a DuniyarYada Labarai da Sadarwa ta Zamani wanda hakan zai kawo cigabaga a Kasata Najeria dama Duniya baki daya.

BURINMU

Burinmu shine samar da rahotanni masu inganci, wadanda za’ayi alfahari dasu a fanninYada Labarai da Sadarwa ta Zamani; wanda hakan zaisa al’umarmu su rinka tunani maikyau wanda hakan zai haifar da cigaba da bunkasar arziki a kasar Najeria dama Duniya baki daya.

MANUFOFINMU

  • Mu kasance daga cikin kafafenYada Labarai masu zaman kansu da suke samar da labarai na gaskiya masu inganci ta hanyar da masu bibiyarmu zasu gamsu da labaran da muke basu.
  • Mu kasance masu sauraron ra’ayoyin masu bibiyarmu ta yarda zamu samar musu da labaran da suka dace da bukatarsu, ba tare da mun kauce daga kan dokoki na gudanar da aikin jarida ba.
  • Samar da labarai cikin hikima da kwarewa wanda hakan ka iya samar da labarai sababbi da zasu burge masu bibiyar mu.

MUHIMMAN LABARAN MU

Irin labaran da zamu bawa muhimmanci sun hada da: Harkar Noma da Kiyo, Lafia, Ilimi, Mahalli, Siyasa, Sadarwa, Kasuwanci, Labarun Ban Mamaki, Nishadantarwa da Wasanni da sauransu.

TARIHIN MAWALLAFI

Aliyu Mudi Sulaiman, ya sami Digirinsa akan Harkar Yada Labarai daga Jami’ar Bayero. Kafin sannan ya sami shedarkammala karatu a  mataki na Diploma a fannoni har guda hudu.

Aliyu ya shafe kusan shekaru Talatin yana aikin Jarida. Yayi aiki da Madabi’ar buga Jaridu ta Triumph dake Kano. Sannan yayi aiki da Kamfanin Media Trust Limited, mamallaka Jaridun Daily/Weekend Trust da kuma Aminiya. Kafin sannan yayi aiki da kananan kamfanonin jaridu da dama.

Har’ila yau yayi aiki da gidan Radio na Express dake Kano da Liberty Radio da Talabijin. Yayi aikin Jarida a gurare da dama a Jahohi harda MajalisarTaraiya da Fadar Shugaban Kasa.

Bangaren da Aliyu yafi sha’awa da  Kwarewa akai shine bin diddigin labarai. Hakan yasa ya rinka samun shafin Farko a jaridun da ya yiwa aiki da kuma kasancewa daya daga cikin masu samar da labarai na daga gaba-gaba a gidajen radio da television da yayiwa aiki.

Burin Aliyu, shine gudanar da aikin jarida a bisa tsari na gudanar da aikin jarida kamar yadda yake a nan Najeria da sauran kasashen duniy; wanda hakan shi zai sa ayiwa Talakawa adalci ta hanyar gudanar da shugabanci na gari. Hakan shi zai samar da zaman lafia da cigaba mai dorewa.