Home Lafiya Shirin Mayar Da Yara Makaranta: UNICEF/EU Sun Kaddamar Da Gangami A Kano

Shirin Mayar Da Yara Makaranta: UNICEF/EU Sun Kaddamar Da Gangami A Kano

84
0
UNICEF logo

Daga: Sulaiman Hussaini D/Kudu

Asusun tallafawa illimi na majalisar dinkin duniya da kungiyar kasashen turawa tare da hadin gwaiwar hukumar illimin bai  daya ta jahar Kano sun gudanar da taron gangamin wayar da kai dangane da shirin mayar da yara makarantu a jahar Kano, da nufin kawu karshen rashin zuwan yara makaranta mai taken “Education And Youth Empowerment Project in Northern Nigeria.

Da take jawabinta yayin bude taron wanda aka gudanar a makarantar sakandiran gwamnati dake Gwammaja a karamar hukumar Dala wakiliyar Asusun tallawa illimin yara  na majalisar dinkin duniya Hajiya Aisha Abdullahi ta bayyana cewa makasudun shirin shine dan kara karfafawa iyayenyara, shuwagabanni kungiyoyi,kungiyoyin mata gwaiwa dan ganin yara na shiga makarantu a wannan zangun karatu na shekara ta 2025/2026. Dama kara karfafawa mahalarta taron gwaiwa wajan tunkarar duk wata matsala dake hana yara zuwa makaranta ko barin makaranta bayan sun fara zuwa.

Acewarta dukkan yara sun cancance zuwa makaranta ” akwai yara da dama da suke ba a makaranta ba saboda rashin wayewa, bukata ta musamman, banbanci jinsi wanda ke kawu raguwar zuwan yara makaranta, wasu kuma wuraran suna fuskantar matsalar barin yaran daga bayan sun fara zawa makarantu.”

Ta kuma kara da cewa kungiyoyi nada muhimmiyar rawar da zasu iya takawa wajan shawu kan wannan matsalar “idan aka sami hadin kai tsakanin kungiyoyi da gwamnati hakan zai mutukar taimakawa wajan kara wayar da kan alumma musammam iyayenyara, masu kula dasu wajan ganin ana sanya idanu dan ganin suna zuwa makarantar akan lokacin kuma  a kuwacce rana.

Babban makasudun wannan taron dai shine samun hanyar magance matsalar rashin kai yara makarantu da  kuma dena zuwansu daga baya. Dama hada kai da kungiyoyin iyaye da malamai na makarantu, kungiyoyin mata dana masu bukata ta musammam da nufin farfadu da harkar illimi a kasar nan musammam bangaran Arewacen kasar nan wanda ake ganin shine kuma baya ta fannin illimi.

Anasa jawabin Wakilin Arewa Alhaji Dalhatu Jibrin godewa irin wadannan kungiyoyi yayi na kasashen wajan ganin yadda suke tiri tiri dan  ganin illimi ya farfadu a kasar nan. Inda yace matsalar gyaran illimi ba abudane da daya ta’allaka akan gwamnati kawaiba sai an hada hannu kuwa ya shigo ciki dan magance wannan matsala musammam iyaye,shuwagabannin al’ummar, sarakunan gargajiya,dan ganin an cetu wannan fanin daga dukushewa.

Dayake tufa albarka cin bakin Shugaban majalisar kansulolin karamar hukumar Dala  Hon. Auwalu Ibrahim Shuaibu nuna farin cikinsu yayi tare da godewa wadannan kungiyoyi ganin yadda suke tallafawa fannin illimi a wannan jaha. Tare da bada tabbacin majalisar karamar hukumar na bada duk wani gudun mawa daka iya tallafawa dan ganin shirin ya dure an sami nasarar da ake bukata.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here