Kwararru su na has ashen cewa Liverpool za ta kara lashe kofin Premier League a bana, bayan da ta lashe na kakar da ta wuce na 20 jimilla iri ɗaya da yawan na Manchester United.
A ranar Litinin aka rufe kasuwar saye da sayar da ƴan ƙwallo a nahiyar Turai, inda Liverpool ce kan gaba a yawan kashe kuɗi da ta sayo ƴan wasa a bana da ya kai fam miliyan 415.
Chelsea ce mai rike da tarihin a 2023, wadda ta sayi ƴan ƙwallo kan fam miliyan 400, kuma Liverpool ta yi kokarin sayen Marc Guehi daga Crystal Palace ranar Litinin kan fam miliyan 35, sai a soke cinikin.
Tun farko an cimma matsaya daga baya Palace ta janye daga cinikin da cewar ba ta samu damar sayen madadinsa ba.
A karo biyu a bana Liverpool ta ɗauki ƴan wasa kan kuɗi mai tsoka a matakin mafi tsada a Burtaniya da ya haɗa da Florian Wirtz daga Bayern Leverkusen kan fam miliyan 100, sai kuma ta sayi Alexander Isak daga Newcastle United kan fam miliyan 125, yanzu shi ne cinikin ɗan wasa mafi tsada a Burtaniya.
Jerin ƴan wasan da suka koma Liverpool a bana:
Giorgi Mamardashvili (Valencia)
Jeremie Frimpong (Bayer Leverkusen)
Armin Pecsi (Valencia)
Florian Wirtz (Bayer Leverkusen)
Milos Kerkez (Bournemouth)
Freddie Woodman (Preston North End)
Hugo Ekitike (Eintracht Frankfurt)
Will Wright (Salford City)
Giovanni Leoni (Parma)
Alexander Isak (Newcastle). (BBC Hausa)





























