Home Siyasa 2027: Yau Shugaba Tinubu Zai Karbi Tutar Tsayawa Takara A Jam’iyar APC

2027: Yau Shugaba Tinubu Zai Karbi Tutar Tsayawa Takara A Jam’iyar APC

7
0
Pres. TINUBU

A yau Lahadi ne shugaba Bola Ahmed Tinubu zai karɓi takardar shaidar jam’iyyar APC a matsayin ɗan takarar shugabancinta a zaɓen 2027.

Kwamitin zaɓen fidda gwani na shugaban ƙasa zai gabatar da takardar shaidar da tutar a cibiyar taro ta ƙasa da ƙasa ta Bola Ahmed Tinubu da ke Abuja bayan tattara sakamakon zaɓen fidda gwani a faɗin ƙasar.

Gwamnonin APC, membobin kwamitin zartarwa na ƙasa, kwamitin aiki na ƙasa, da majalisar dokoki ta ƙasa, tare da jiga-jigan jam’iyyar, za su halarci taron.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here