Home Uncategorized ‘Yadda cin zali a makaranta ya yi ajalin ‘yata’

‘Yadda cin zali a makaranta ya yi ajalin ‘yata’

234
0
Cinzali a Makaranta mata

Yau 2 ga watan Nuwamba ake gangamin yaƙi da cin zarafi ko kuma cin zali a makarantu.

Hukumar bunkasa ilimi da al’adu ta Majalisar Dinkin Duniya, UNESCO ce ta ayyana duk ranar Alhamis ɗin farko ta watan Nuwambar kowacce shekara a matsayin ranar yaƙi da cin zarafi da cin zali a makarantu.

Kuma ciki har da nau’in cin zalin da ake yi ta sabuwar hanyar rayuwa ta intanet, da da manufar kawo ƙarshen tarzoma a makarantu don inganta lafiyar ƙwaƙwalwar yara da koyon iliminsu.

BBC ta samu zantawa da wata uwa wadda ta ce garin irin wannan cin zarafi ta rasa ‘yarta bayan kwashe shekaru suna jinya an gaza gano abin da ke damunta.

Mahaifiyar mai suna Hauwa Ahmad Aminu da ke jihar Kano a arewacin Najeriya ta ce sanadin wannan lamari da ya faru da ‘yarta ne ya ja ta kafa gidauniya inda ta ke wayar da kai game da cin zalin yara a makarantu.

“Ba duka ake magana ba in aka ce cin zali a makaranta, ko kuma idan aka ce cin zarafi, a zaci ta hanyar lalata.

“Magana ake ta faɗawa yaro ko yarinya magana da za ta yi masa tasiri a kwakwalwa, ta janyo masa koma baya wajen fahimta da saurin koyo.

“A mafi yawan lokuta kalmomin ne na muzantawa, ta hanyar suffofin halittarsu ko iyalansu ko kuma ƙoƙarinsu a makaranta,” in ji Hauwa Ahmad.

A cewarta idan abubuwan suka ta’azzara yara suna shiga yanayin damuwa kuma hakan kan shafi kwakwalwarsu.

‘Duk wanda ya yi makaranta ya taɓa fuskantar matsalar’

A cewar wanan mahaifiya matsalar cin zali ko cin zarafi a makarantu babba ce, domin kuwa ta zama wata ɗabi’a tsakanin ɗalibai.

“Duk wanda ya yi makaranta ya san tsananin tasirin wannan matsala, abin da ya sa ba a nuna damuwa sosai a kai shi ne, ƙarancin tasirin matsalar tsakanin yara a baya.

“Amma a yanzu wannan abu na tasiri kuma har ya haifar musu da koma baya a ɓangaren koyo,” in ji Hauwa.

Irin waɗannan kalaman muzantawa na fitowa daga bakin malaman yaran a wasu lokutan, a matsayin hukunci idan sun yi musu laifi, in ji ta.

Malami kan iya kallon yaro su ce masa “mai kunnuwa kamar fanke” shi kenan daga nan sai ɗalibai ‘yan uwansa su ɗauka.

Dole sai suma malamai sun kiyaye irin wannan kalaman da illar da suke yi.

‘Shekaru muka yi muna jinyarta, ta mutu daga ƙarshe’

Hauwa ta ce lokacin ‘yarta na aji ukun farko na sakandire sai aka yi mata shugabar dalibai, abin da ya haifar da kishi tsakaninta da wata abokiyar karantunta.

Wannan yasa ita abokiyar tata ta gama kai da wasu kawayenta irin ‘marasa jin nan’ wannan ya sa suka riƙa yi mata barazana da rayuwarta.

Hakan ya haifar mata da tsoro kuma ya sa ta shiga tsananin damuwa, har ta zo ta fara jijjiga.

“Shekara bakwai muka kwashe muna zuwa asibiti, duk inda muka je sai a ce damuwa ta riga ta yi mata illa a kwakwalwarta. Daga nan kwakwalwar ta fara shanyewa har ta yi sanadiyyar rayuwarta”.

Mahaifiyar ta ce ba su kai ga gano wannan matsala da ruwi ba balle su sauya wa ‘yar tasu makaranta ko kuma su kai koke ga hukumomi.

Sai da aka kwashe shekara biyu tana haɗiyar wannan damuwa da baƙin ciki, ba ta faɗa ba balle a san halin da take ciki saboda tsoro.

“Randa abin ya bayyana suma ta yi, sai da ta yi kwana biyar a sume, ba a san me ya sameta ba.

“Da ta farka likita ya ce mata Zainab barka da farfaɗowa, sai ta cewa likitan ba ta son ta mutu, sai ya ce wanene ya ce za ki mutu?, sai ta sake suma,” in ji mahaifiyar.

A cewar mahaifiyar ta shiga damuwa kafin mutuwarta yawanci abin yakan fara mata da matsanancin ciwon kai, sai ka ji ta kwalla kara shi kenan.

“A matsayina na uwa ko me zan faɗa mutane ba za su gane raɗaɗin da na ke ji ba na tsawon wannan shekaru tun bayan mutuwarta.

Ta bai wa iyaye shawarar riƙa jan yaransu a jiki ta yadda za su sake da su, su riƙa shaida masu damuwarsu kan abin ya ta’azzara.

Ta ce da an ga yaro baya shiga cikin ‘yan uwansa yara kamar wanda ake tsangwama, to a yi maza a ji meke damun shi.

Iyaye su kasance masu nazarin halayyar ‘ya’yansu ta yadda da sun sauya za su iya maza su fahimta.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here