Home Siyasa Majalisar Dattawa Ta Bukaci Gwamnatin Najeriya Da Ta Dawo Da Karbar Haraji...

Majalisar Dattawa Ta Bukaci Gwamnatin Najeriya Da Ta Dawo Da Karbar Haraji A Iyakokin Tsandauri

344
0
20230719 142259

Majalisar Datttawa ta bukaci gwamnatin Taraiya da ta janye dokarnan da ta tiliasta biyan kudin fito a Tashar Jiragen ruwa ta Lagos a maimakon haka a rinka biyan kuddqden fito a dukkan iyakoki na tsandauri.

Dan majalisar Dattawa mai Wakiltar Katsina ta tsakiya Abdul’aziz Yar’adua ne ya gabatar da wannan bukatar ta gaggawa a zauren Majalisar ran Laraba ganin yadda jami’an Hukumar Hana Fasa kauri wato Kwastam su ke hallaka rayukan mutane a yankin sa.

Ya ce, abun ya kai har shugaban Ma’aikatan Gwamnatin Jihar Katsina su ka budewa wuta tare da shi da iyalinsa a karshen makon da ya gabata.
Sanata Yar’adua ya ce hakan ya sabawa dokar rike bondiga a dukkan hukumomin tsaro da ke kasarnan.
” a matsayina na tsohon soja nasan a kwai ka’idoji da ake bi kafin a yi harbi. Sa bo da haka sai idan ya zama dole ko kuma wanda aka tare ya fito da bindiga sannan sai suyi kokarin kare kansu”.
Ya kara da cewa jami’an Kwastam sun  hallaka mutane da yawa akan shigo da shinkafa buhu daya kachal a sakamakon dokar da ta ba su damar yin harbi a gwamnatin da ta shude.
 Yar’adua ya ce Majalisa ta 10 za ta ne mi da a cire wannan doka domin ta sabawa yancin dan adam.
Dan Majalisar ya ce an hana dubunnen mutane sana’a a yankin iyakar Jibiya da Daura sakamaon ha na shigo da kayayyaki ta iyakar tsandauri.
Sa bo da haka Majalisar za ta bukaci da a saka haraji kamar yadda yake a tashoshin ruwa domin ya bawa mutane dama su ci gaba da harkokin su na kaswanci ba tare da musgunawa ba.
Bayan haka Dan Majalisar ya ce Majalisar ta kafa Kwamiti domin ya binciki abubuwan da suke faruawa a iyakokin tare da neman Hukumar Kwastam da ta biya diyyar mutanen da ta kashe kamar yadda aka taba yi a baya.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here