Home Lafiya Wata Kungiyar Likitoci Zata Yiwa Mutane 500 Kyauta A Kano

Wata Kungiyar Likitoci Zata Yiwa Mutane 500 Kyauta A Kano

41
0

Daga: Suleiman Hussaini Do/Kudi

Ana sa rain a kalla mutane dari biyarne zasu amfana da shirin aikin gyraran idanu kyauta a Kano a wani bangare na bikin ranar likitocin ido wanda ake gabatar dashi duk shekara.

Kamar yadda shugaban kwamatin tsare tsare na kaddamar da shirin na kungiyar likitocin ido ta kasa reshen jahar Kano Dr. Umar Faruq Ibrahim ya bayyanawa manema labare a asibitin kuyarwa na Aminu Kano.

Dr. Faruq yace wannan aikin ana gudanar dashine hadin gwaiwa tsakanin kungiyar ta likitocin ido da wata kungiya mai suna AMA Foundation sai wani asibiti Sight Boost dake nan Kano. Inda yace ita kungiyar ta AMA Foundation su za suyiwa mutane dari hudu a asibitin kuyarwa na Aminu Kano

inda shi asibitin na Sight Boost zasu yiwa mutane dari Daya a asibitin kwararro na Murtala Muhammad.,ya kuma jaddada cewar wannan aikin gaba daya kyauta aka gudanar dashi tun daga farkon karbar katin har zuwa karbar magunguna wasu kuma sai an musu aiki.”shi wannan aikin kyautane inda kungiyar

Ama Foundation da Sight Boost Hospital sune suke bayan kudin aikin da magunguna mikuma a matakin kungiya muka samar da likitoci”.

A karshe Dr Umar Faruq yayi kira ga wadanda suka amfana da shirin na aikin idanu kyauta da suyi amfani da magungunan da aka basu kamar yadda likitocin sukai sukai musu bayani tare da gujewar duk wani abun da zai sa aikin nasu lalacewa ga wadanda aka yiwa aiki.

Malam Abdullahi Inusa na daga cikin wadanda suka amfana da aikin idanun kuma muka tattauna dashi inda ya nuna farin cikinsu tare da yiwa wadannan kungiyoyi godiya da fatan alkhairi dange ne da wannan namijin kukari da sukayi.

Taken taron na baka dai shine “Ilimi da kuma Kuyarwa”.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here