,Mataimakin Shugaban Majalisar Dattawa, Sanata Barau I. Jibrin, ya kaddamar da rabon buhun taki guda 37,880 kyauta ga manoman jihar Kano a Wani yunkuri Na wadata Kasa da abinci.
An fara rabon ne a ranar Lahadi a kananan hukumomin da ke shiyyar Kano ta Arewa, kamar yadda mai ba shi shawara kan harkokin yada labarai, Ismail Mudashir ya bayyana.
Sanata Barau, wanda ya saba raba taki ga manoma a kowace shekara, ya ce wannan shiri na da nufin tallafa wa kokarin Gwamnatin Tarayya na cimma isasshen abinci a ƙasa. A yayin bikin kaddamarwar da aka gudanar, wanda Shugaban Ma’aikatansa, Farfesa Muhammad Ibn Abdallah, ya wakilta shi, ya ce: “Wannan taki kyauta ne gaba ɗaya. Babu wani manomi da za a bukaci ya biya ko sisin kobo.”
Ya kara da cewa, “Manoma su ne ginshiƙi a karkara, kuma ba don da su ba, ba za mu samu abinci ba. Wannan matakin zai taimaka matuƙa wajen bunkasa noma da samun wadataccen abinci.” Sanatan ya kuma tabbatar da ci gaba da aiki tare da hukumomi domin samar da ci gaba ga fannin noma a Kano da ma fadin Najeriya.

Wasu daga cikin manoman da suka amfana da wannan shiri sun bayyana godiyarsu ga Sanata Barau, inda suka ce ya kasance jagora na gari da ke tsaya musu a koda yaushe.
Mallam Ibrahim Musa Bagwai ya ce, “Sanata Barau jagora ne mai daraja. Kowace shekara yana ba mu taki domin mu samu albarkar noma. Allah ya saka masa da alheri a duniya da lahira.”





























