Home Siyasa Sanata Ali Ndume Ya Kalubalanci Rabawa Yan Najeriya Miliyan 12 Naira 8,000

Sanata Ali Ndume Ya Kalubalanci Rabawa Yan Najeriya Miliyan 12 Naira 8,000

221
0
Sen. Ndume

Sanata Ali Ndume Dan Majalisar Taraiya da ga Jihar Borno ya kalubanci shirin Gwamnatin Taraiya na rabawa Yan Najeriya mutum miliyan 12 naira duba takwas a wani mataki na rage radadin cire tallafin man fetur da akayi.

Sanata ya nuna rashin amincewar sa da wannan tsari ne a hirarsa da Yan Jaridu a ofishinsa da ke Majalisar Dattawa da ke Abuja a ranar Talata in da ya ce hakan ba zai haifar da da mai ido ba.

Ya ce a maimakon a rabawa gidaje ko mutane miliyan 12 naira 8,000 kamata ya yi a yi amfani da kudin domin bayar da tallafi ga manoma na taki ko kayan noma ko kuma a sayi motoci a raba ga kananan hukumomi 774 domin tallafawa wajen zirga zirga a farashi mai sauki.

Ndume ya ce fito da tsari irin wadan nan su ne za su iya rage radadi da Yan Najeriya suke fuskanta amma raba N8,000 ga gidaje Miliyan 12 bazai rage radadin komai ba.

“ ta ya ya za a iya ware gidaje da suka fi kowanne talauci a Najeriya. Kuma ana maganar gidaje ko mutum miliyan 12 a cikin sama da mutum miliyan 200. To su kuma sauran fa? Bayan haka idan an zo biyan wadan nan bashi Mutum Miliyan 200 za su biya bashin da mutum miliyan 12 suka amfana. A kwai adalci a wannan tsari?  Ndume ya tambaya.

Sanata Ndume ya kara bayani cewa ya na da masaniya cewa  Bankin Duniya wato “World Bank” ne ya bayar da bashin Dalar Amurka Miliyan 800 kuma ya bayar da cewa ga yadda za a kashe bashin.

Sai dai, ya ce Naira Biliyan 500 da Majalisar Taraiyar ta amince da shi da ga cikin Kwarya- kwaryar kasafin kudin shekara ta 2023 a ka samar da su sabo da haka Shugaban Kasa, Bola Ahmad Tinubu zai iya fito da tsari da ya ke ganin zai amfani Yan Najeriya ya yi amfani da shi wajen rabawa.

Sanata ya ce Majalisar za ta yi iyakacin kokarinta wajen ganin ta bibiyi yadda za a kasafta kudin ga Yan Najeriya musamman Naira Biliyan N500 da su ka saka a cikin Kwarya – kwaryar Kasafin Kudi na shekara ta 2023.

A wani bangare kuma Sanata Ndume ya tabbatar da cewa gaskiyane an ware kudade a cikin kasafin kudin domin saya musu motoci na alfarma da sauran kayayyaki da suke bukata a ofisoshin su kamar su komfuta da sauran kayan aiki.

“Wannan ba wani sabon abu bane. Duk lokacin da aka kafa sabuwar Majalisa ana sayawa Yan Majalisar Motoci da sauran kayayyakin aiki tun shekara ta 1999 har ya zuwa yan zu haka tsarin yake” inji Ndume.

Sanatan ya ce motocin su na yin amfani da su ne wajen gudanar da aiyukan Majalisa da kuma zagaye na mazabun su. Inda ya ce su kuma su kwamfuta da na’urar foto kwafi da sauransu su na yin amfani da sune domin gudanar da aikin ofis.

 

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here