Home Noma da Kiwo Takin Zamani: Dangote Ya ƙaddamar Da Aikin Gina Kamfani Na Biliyan 2.5...

Takin Zamani: Dangote Ya ƙaddamar Da Aikin Gina Kamfani Na Biliyan 2.5 A Habasha

130
0
Dangote Gode Fertilizer Habasha

A yunkurinsa na ganin ya bunkasa samar da takin Zamani a Kasashen Afrika Shugaban Rukunin kamfanoni na Dangote, Aliko Dangote ya ƙaddamar da fara aikin gina kamfanin takin zamani mai suna Dangote Gode Fertilizer a ƙasar Habasha.

 

Kamfanin zai lashe Dalar Amurka Biliyan 2.5 a kasar Habasha. Kafin wannan Dangote ya taba kaddamar da irin wannan  Kamfani na irin wadannan kudade a Ibeju Lekki da ke Jihar Legas a Najeria.

 

Aliko y ace manufar samar da wadanan kamfanunnuka shine samar da taki wanda zai taimaka wajen wadata kasashen Africa da abinci mai kyau da arha.

 

Shugaban rukunin kamfanonin, Alhaji Aliko Dangote ne da kansa ya jagoranci ƙaddamar da fara aikin gina kamfanin mai suna Dangote Gode Fertiliser Plant a ƙasar Habasha.

 

Daga cikin waɗanda suka samu halartar ƙaddamar da fara aikin, akwai Firaministan Habasha, Abiy Ahmed da shugaban kamfanin man fetur na MRS, Sayyu Dantata da shugaban rukunin kamfanonin NGX, Umaru Kwairanga da shugaban kamfanin hannun zuba jari na Habasha, Biru Taye. (BBC).

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here