Daga: Suleiman Hussaini D/ Kudu
Kungiyar likitocin ido ta kasa reshen jahar Kano ta kuduri niyyar yiwa mutane dari biyar (520) aikin gyraran idanu kyauta a wani bangare na bikin ranar likitocin ido ta duniya wanda ake gabatar da shi duk shekara.
Shugaban kwamatin tsare tsare na Kungiyar ne Dr. Umar Faruq Ibrahim ya kaddamar da shirin na kungiyar likitocin ido ta kasa reshen jahar Kano ya ya bayyanawa manema labare a asibitin koyarwa na Aminu Kano.
Dr. Faruq yace taken taron na bana dai shine “Ilimi da kuma Koyarwa” kuma wannan aikin ana gudanar da shine hadin gwaiwa tsakanin kungiyar ta likitocin ido da wata kungiya mai suna AMA Foundation sai wani asibiti Sight Boost dake nan Kano.
Inda yace ita kungiyar ta AMA Foundation su za su yiwa mutane dari hudu a asibitin koyarwa na Aminu Kano inda shi asibitin na Sight Boost za su yiwa mutane dari Daya a asibitin kwararru na Murtala Muhammad.
Ya kuma jaddada cewar wannan aikin gaba daya kyauta ake gudanar da shi tun daga farkon karbar katin har zuwa karbar magunguna wasu kuma sai an musu aiki.”shi wannan aikin kyautane inda kungiyar Ama Foundation da Sight Boost Hospital su ne su ke biyan kudin aikin da magunguna su kuma a matakin kungiyar mu samar da likitoci”.
A karshe Dr Umar Faruq ya yi kira ga wadanda su ka amfana da shirin na aikin idanu kyauta da su yi amfani da magungunan da aka basu kamar yadda likitocin sukai mu su bayani tare da gujewa duk wani abun da zai sa aikin na su lalacewa ga wadanda aka yiwa aiki.
Malam Abdullahi Inusa na daga cikin wadanda su ka amfana da aikin idanun kuma ya nuna farin cikin sa tare da yiwa wadannan kungiyoyi godiya da fatan alkhairi danga ne da wannan namijin kokari da su kayi.





























