Cristiano Ronaldo ya sake zama kan gaba cikin jerin ƴanwasan da aka fi biya a duniya.
Shekara uku a jere kenan ɗan wasan na Portugal na samaun wanann matsayi, da fitacciyar mujallar nan da ke ƙiyasin dukiya ta Fobes.
Mujallar ta ce sau biyar Ronaldo yana samun matsayin a sana’arsa ta ƙwallon ƙafa, inda ta ƙiyasta kudin da aka biya ɗan wasan da kimanin dala miliyan 275.
Adadi kudin da ɗan wasa ɗaya ne a tarihi ya taɓa zarta su, wato ɗan wasan dambe ne duniya, Floyd Mayweathe, wanda a 2015 a ysamu kimanin dala miliyan 300.
A watan Disamban 2022, Ronaldo mai shekara 40 ya koma ƙungiyar Al Nassr ta Saudiyya a wani ciniki mai gwaɓin gaske.
Mujallar ta ce ɗan wasan ya samu kuɗi sakamakon wasu tsarabe-tsarebe da yarjejeniyarsa ta ƙunsa da kuma wasu tallace-tallace da kuma yawan mabiya a shafukansa na sada zumunta, da a yanzu suka kai miliyan 939.
Ƴanwasa 10 da aka bi biya a duniya a 2025
Cristiano Ronaldo, ƙwallon ƙafa dala miliyan 275
Stephen Curry, ƙwallon kwando, dala miliyan 156m
Tyson Fury, wasan dambe dala miliyan 146
Dak Prescott, ƙwallon ƙafa dala miliyan 137
Lionel Messi, ƙwallon ƙafa dala miliyan 135
LeBron James, ƙwallon kwando dala miliyan 133.8
Juan Soto, kwallon baseball dala miliyan 114
Karim Benzema, ƙwallon ƙafa dala miliyan 104
Shohei Ohtani, ƙwallon baseball dala miliyan 102.5
Kevin Durant, ƙwallon kwando dala miliyan 101.4





























