Majalisar Dokokin Jihar Kano ta dakatar da shugabannin ƙananan hukumomin Bagwai, Bebeji da Rogo daga bakin aikinsu na tsawon watanni uku domin ba da damar gudanar da bincike kan zarge-zargen almundahana da kuɗaɗen al’umma da ake yi musu.
Masaki Hausa TV ta rawaito daga Siyasarmu TV cewa, Jami’in Yaɗa Labaran Majalisar Dokokin Jihar Kano, Malam Kamaluddeen Sani Shawai, ya tabbatar da matakin da majalisar ta ɗauka.
Shugabannin ƙananan hukumomin da abin ya shafa sun haɗa da Alhaji Bello Abdullahi Gadanya na Bagwai, Dr. Alhassan Salisu na Bebeji da Alhaji Abubakar Mustapha Rogo na Rogo.
A cewarsa, matakin ya biyo bayan karɓar rahoton kwamitin bincike da majalisar ta kafa domin duba ƙorafe-ƙorafen da ƙungiyoyi da al’ummomin ƙananan hukumomin suka shigar kan shugabanninsu, inda ake zarginsu da badaƙalolin almundahana da kuɗaɗen jama’a.
- An ce dakatarwar za ta ba da damar gudanar da cikakken bincike kan zarge-zargen da ake y






























