Home Tsaro Katsina: Yadda DSS Da ‘Yan Sa-kai Su Ka Kashe Fitaccen Jagoran ‘Yan...

Katsina: Yadda DSS Da ‘Yan Sa-kai Su Ka Kashe Fitaccen Jagoran ‘Yan Bindiga Da Mayaƙansa Sama Da 60

7
0

A Arewa maso Yammacin Najeriya, jami’an DSS tare da haɗin gwiwar masu sa-kai na al’umma da ƙwararrun mafarauta a Jihar Katsina sun kashe sama da mutum 60 a wani gagarumin samame na jami’an Hukumar Tsaro ta Farin Kaya (DSS) bisa ingantattun bayanan sirri ya yi wa ayyukan ‘yan bindiga mummunar illa ‘yan bindiga ne, ciki har da fitaccen jagoran masu garkuwa da mutane, Idi Abasu Aiki, a wani kazamin artabu a Ƙaramar Hukumar Bakori.

A rahoton da jaridar Tribune ta wallafa, ta bayyana cewa, majiyoyin tsaro sun ce Idi Abasu Aiki, wanda aka daɗe ana kallonsa a matsayin ɗaya daga cikin manyan jagororin ‘yan bindiga mafi hatsari a Katsina da maƙwabciyarta Zamfara, yana cikin waɗanda aka kashe a samamen da aka shirya bisa sahihan bayanan sirri.

A cewar majiyoyin, sama da ‘yan bindiga 200 masu ɗauke da manyan makamai, ƙarƙashin jagorancin Idi Aiki tare da goyon bayan mayaƙan da ke da alaƙa da fitaccen jagoran ‘yan bindiga Ado Aleru na Zamfara, sun kai farmaki ƙauyen Guga domin ɗaukar fansa kan al’ummomin da suke zargin suna ba jami’an tsaro da masu sa-kai bayanan sirri.

An ce manufar harin na ‘yan bindigar shi ne, kashe jami’an tsaron al’umma da mafarautan da suka yi wa ƙungiyoyin ‘yan bindiga mummunar illa a wani artabu da aka yi a baya a ƙauyen Dawan Laila da ke Bakori, inda aka kashe sama da ‘yan bindiga 40.

Sai dai ba tare da sanin ‘yan bindigar ba, jami’an tsaro sun riga sun samu bayanan sirri kan shirin harin, inda suka shirya dakarunsu domin yi musu kwanton ɓauna.

Wata majiyar tsaro ta ce, “‘Yan bindigar sun faɗa tarkon da aka shirya musu. DSS ta samu sahihan bayanai tun kafin harin, sannan ta haɗa kai da masu sa-kai da mafarauta. Sama da ‘yan bindiga 60, ciki har da Idi Abasu Aiki da aƙalla manyan kwamandojinsa 14, an kashe su a artabun.”

Sai dai duk da nasarar da aka samu, an rasa rayukan mutum huɗu daga cikin masu sa-kai da mafarautan da suka taimaka wa jami’an tsaro a yayin fafatawar.

Bayan kammala artabun, jami’an tsaro sun gudanar da aikin share fage a yankin, inda suka kwato makamai da sauran kayayyakin da ‘yan bindigar suka bari yayin da suke guduwa (Leadership Hausa).

 

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here