Home Siyasa An Bukaci Yan Najeriya Da Su Rungumi Yafiya Maimakon Gaba Don Kasancewa...

An Bukaci Yan Najeriya Da Su Rungumi Yafiya Maimakon Gaba Don Kasancewa Tsintsiya Madaurinki Guda – Sanata Shekarau

87
0
SHEKARAU @70

Sanator Ibrahim Shekarau, Tshohon Gwamnan Kano kuma Ministan Ilimi  ya bukaci ‘yan Najeriya da su rungumi yafiya da zaman lafiya,  a maimakon gaba domin kasancewa kasa daya al’umma daya a wani mataki  na derewar cigaban Kasarnan.

Shekarau wanda ya cika shekaru 70 a duniya a makon nan, ya bayyana hakan ne yayin ganawa da manema labarai a Kano a wani ɓangare na shagulgulan bikin cikar sa shekaru 70 da haihuwa.

Ministan wanda ya yabawa Yan Najeriya da irin hadin kai da suka nuna tsakanin kiristoci da Musulmi musamman ganin yadda suka mayar da martini na kalaman Shugaban Kasar Amurka Donald Trump.

Ya shawarci Shugaban Kasa, Bola Ahmad Tinubu daya rungumi tattaunawa game da kalaman na Shugaba Trump domin gujewa fadawa wata matsala da ka iya jefa kasar cikin wani hali.

A wani bangaren Shekarau yace  ya yafe wa duk wanda ya taɓawa ɓata masa rai, tare da neman gafara daga waɗanda shi ma ya ɓata wa rai.

“Na yafe wa duk wanda ya taɓa ɓata min rai, ko na sani ko ban sani ba. Ina roƙon Allah Ya karɓi yafiyata,” in ji shi.

 

Tsohon Gwamnan Jihar Kano kuma Tshohon  Sanata wanda ya wakilci Kano ta Tsakiya, Shekarau, ya ce siyasa ta zama wani ɓangare na rayuwarsa, kuma ba zai daina shiga harkar siyasa ba muddin yana da ƙarfi da lafiya

Ya ce dalilin da yake sa shi ci gaba da kasancewa cikin harkokin siyasa shi ne kishin ƙasa da kuma burin ganin an samu shugabanci nagari mai cike da gaskiya da adalci.

 

“Siyasa wani ɓangare ne na rayuwata. Matukar ina da lafiya da ƙarfi, zan ci gaba da bayar da gudunmawa wajen samar da shugabanni nagari. Ba zan taɓa barin siyasa ba,” in ji shi.

Shekarau ya ce bai taɓa shiga siyasa don neman kuɗi ko matsayi ba, illa kawai don hidima ga jama’a da ƙoƙarin tabbatar da shugabanci mai rikon amana.

“Ba don amfanin kaina na ke siyasa ba. Burina shi ne in tallafa wa shugabanci da ya ginu kan gaskiya da adalci,” in ji shi.

 

Tsohon gwamnan ya bayyana godiyarsa ga Allah bisa tsawon rayuwa da Ya ba shi, daga aikin malanta zuwa rike muƙamai daban-daban kamar gwamna, minista da sanata.

“Na gode wa Allah da Ya ba ni damar rayuwa mai tsawo da hidima a fannoni daban-daban. Shekaru 70 a rayuwa babbar ni’ima ce,” in ji shi.

Shekarau, wanda ya mulki Jihar Kano daga 2003 zuwa 2011, ya rike muƙamin Ministan Ilimi a gwamnatin tarayya, sannan ya  wakilta ce Kano ta Tsakiya a Majalisar Dattawa.

 

Ya gode wa iyayensa, malamai, abokai da magoya bayansa bisa irin rawar da suka taka a rayuwarsa, yana mai cewa zai ci gaba da amfani da rayuwarsa wajen hidima ga al’umma.

“Rayuwa gajeriyar lokaci ce. Kowace rana bayan shekara 70 wata ƙarin ni’ima ce daga Allah, kuma zan yi amfani da ita wajen ci gaba da hidimar ɗan Adam,” in ji shi.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here