Home Zirga zirga Badakalar Jiragen NCAT, Zaria: Majalisar Wakilai Ta Gaiyaci Tsohon Ministan Sufurin Sama,...

Badakalar Jiragen NCAT, Zaria: Majalisar Wakilai Ta Gaiyaci Tsohon Ministan Sufurin Sama, Sirika, Rakta Da Su Baiyana A Gabanta

165
0
IMG 20240121 WA0062
  1. Majalisar Wakilai ta bukaci tsohon Ministan Sufurin Jiragen Sama Hadi Sirika da tsohon Rakta Kwalajen NCAT da su baiyana a gabanta ranar Laraba mai zuwa domin su amsa tuhume tuhume game da sayar da wasu jirage guda biyu da aka sayar ba bisa ka’ida ba.
Kwamitin Majalisar mai kula kaddarorin Gwamnatin Taraiya  ne ya bayar da umarnin gaiyatar Ministan da Raktan a wani zama da Kwamitin ya yi ranar Laraba a zauren Majalisar.
Shugaban Kwamitin, Hon.Ademorin Kuye ya ce baiyanar Tsohon Ministan da Raktan a gaban Kwamitin ya zama wajibi domin su amsa tambayoyi  yaddda aka sayar da jiragen ga wasu kamfanoni masu zaman kansu duk da cewa hukumomin Soja da Yansandan da na Soji sama sun nuna bukatar su akan jiragen.
Hon. Kuye ya kara da cewa sun lura da cewa ba a bi ka’idoji ba na sayar da kadarorin gwamnati domin da ga sayen jiragen sababbi da lokacin da aka sayar da su shekaru biyu ne kawai a maimakon shekaru biyar da ya ke a doka Kasa.
Bayan haka kudaden da aka sayar da jiragen da aka saya Dalar Amurka Miliyan 2.4 an sayar dasu akan kudade Dalar Amurka dubu 500 da 600 da yan doriya sayarwace ta wulakanci da Kwamitin bai amince da ita ba.
Daya da ga cilin yan Kwamitin Hon.Isa Muhammad Anka Wanda ya yiwa Yan jaridu karin haske akan batum ya ce ba zata sabu ba, bindiga a ruwa domin Kwamitin na su ya kuduri niyyar ganin cewa an hukunta duk wadanda su ke da hannu akan sayar da jiragen.
Ya cigaba da cewa duk da ya ke shi sabon dan Majalisar Taraiya ne ya gamsu da zummar Kwamitin na cewa baza ayi abum da aka saba yi a baya ba na jingine rahoton Kwamitin baya an kammala bincike.
Hon. Anka ya kara da cewa sun lura da cewa kamfanonin da suka sayi jiragen da kwararren da aka dauka don ya duba jiragen kafin a ssyar da su dukannin su ba su da cikakkun takardun da su ka kamata.
Ya kara da cewa bayan gaiyatar Ministan, Kwamitin ya gaiyaci tsohon Rakta na Kwajen don wanda ya ke kai a yanzu ya gaza amsa wasu tambayoyi duk da cewa yana mataimakin  Rakta lokacin da aka sayar da jiragen.
A yayin gudanar da binciken an sami bayanai masu karo da juna na kudaden da aka sayar da jiragen da kudin da aka biya kwararren da ya jagoranci sayar da jiragen tare da a wadan ne irin kudaden aka sayar da biya kudin jiragen.
Jiragen mallakar Kwalejin Kayar da Aikin Jiragen Sama wato ” Nigerian College of Aviation and Technology,  (NCAT), Zaria an saye su me sababbi domin yin amfani da su domin koyar da daliban makarantar amma aka sayar da su ga wa su kamfanoni masu zaman kansu duk da cewa hukumomin Soja da Yansandan da na Soji sama sun bukaci a  basu su.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here