Home Zirga zirga Majalisar Dattawa Ta Bukaci Gwamnatin Taraiya Da Ta Dawowa Da Tashar Jirgin...

Majalisar Dattawa Ta Bukaci Gwamnatin Taraiya Da Ta Dawowa Da Tashar Jirgin Sama Na Maiduguri Zirga-zirga Na Kasa Da Kasa

140
0
Sen. Ndume 2

Majalisar Dattawa ta bukaci Gwamnatin Taraiya da ta maidawa Tashar Jirgin Sama na Muhammadu Buhari da ke Maiduguri zirga-zirga na Kasa da Kasa kamar yadda ya ke a baya domin bunkasar yankin.

Majalisar ta bayar da wannan umarni ne bayan da Dan Majalisar Dattawa da ga Yankin, Sanata Ali Ndume ya ne mi Majalisar da ta umarci Gwamnatin Taraiya da ta dawo da zirga zirga jiragen na sama na kasa da kasa ya zuwa yankin kamar yadda ya ke a baya.

Dan Majalisar ya ce da wo da zirga zirga zai taimaka wajen ganin an kara samun cikakken tsaro da yalwatar arziki mai yawa a yankin kamar yadda ya ke a baya.

Ndume ya ce dalilin sa na gabatar da wannan bukata ita ce ya lura cewa dukkan yankunan kasarnan guda uku suna da tashar Jirgin sama na Kasa da kasa a Yankin su amma babu a Arewa maso Gabas mai Jihohi 6 wadda Maiduguri it ace helkwatar  su.

Bayan haka ya ce dukkan Jiragen da su ke zirga zirga zuwa kasashen Gabas ta Tsakiya sai sun bi ta Maiduguri ta sama sabo da haka su ka ga chanchantar cewa ya kamata a dawo da zirga zirga a tsahar ta Maiduguri kamar yadda ya ke a baya.

Har ila yau, ya bayar da tabbacin cewa za a samu pasinjoji masu yawa da ga Jihohi guda shida da su ke yankin, harma da wasu kasashen makwabta kamar Chadi da Camaru muddin aka fara zirga zirga a yankin domin yafi mu su kusa domin zuwa kasashen dake Yankin Larabawa.

Majalisar ta Dattawa ta umarci Ministan Sufurin Jiragen sama da ya fara shirye shirye wajen ganin an dawo da zirga zirga a tashar. Kuma ta umarci Kwamiti mai kula da Sufurin Jigagen Sama da ya yi bibiya wajen ganin an dawo da zirga zirgan cikin kankanin lokaci.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here