Home Sadarwar Zamani Laifuffukan Yanar Gizo: Majalisar Dattawa Ta Umarci Kwamitocinta Da Su Karfafa Dokar...

Laifuffukan Yanar Gizo: Majalisar Dattawa Ta Umarci Kwamitocinta Da Su Karfafa Dokar Fasahar Zamani

168
0
Sen. Buba

Majalisar Dattawa ta umarci Kwamitin Fasahar Zamani (ICT) da na Samar da Muhimman Bayanai (Interligence) da su zurfafa bincike wajen ganin sun karfafi dokar kula da Fasahar Zamani domin inganta tsaro da samar da Karin kudaden shiga ga kasarnan.

Majalisar ta bayar da wannan umarni ne bayan da Dan Majalisar Taraiya Mai Wakiltar Bauchi ta Kudu Sanata Shehu Buba Umar da ya gabatar da wani kuduri na gaggawa wanda ya bukaci da ayi gyara akan Dokar domin a karfafa tsaro da samar da Karin kudaden shiga ga kasarnan.

Sanata Buba ya ce ya yi bincike akan kudurin da aka amince da shi akan Tsaro a Yanar Gizo a shekara ta 2015 amma ya lura cewa Dokar ba’a fadada tunani akanta ba wajen ganin ya samar da dokoki a fannoni da dama, sabo da haka ne ya nemi da ayi gyara wajen ganin an shigar da muhimman bayanai.

Ya ce ana amfani da Yanar Gizo wajen aiwatar da manya laifuffuka a duniya dama Najeria irin su damfara iri-iri ta makuden kudade da zamba cikin amince kai harma da kisa amma Kudurin bai lura da kyau da wadannan bangarori ba.

Bayan haka ya ce ya lura cewa manyan kamfanoni masu ta’ammali da harkar Yanar Gizo musamman kamfanonin waya ba sa biyan harajin da ya kamata su rinka biya ga Gwamnatin Taraiya sabo da haka idan akayi gyara a Dokar zai tilasta su su rinka biyan digo biyar na abun da suka samu a Yanar Gizo.

Har ila yau, ya lura cewa mutane da ga kauyen kayau ma su na amfani da Yanar Gizo domin gudanar da harkoki iri-iri ta hanyar amfani da wayoyin su wajen Whatsup da Facebook da sauran manhaja daban-daban don haka akwai bukatar suma a kare mu su hakkin su.

Majalisar Dattawa ta amince da dukkan bukatun da Kudurin ya nema da ayi in da ta umarci kwamitocin guda biyu da su je su hada kai wajen ganin sun samar da ingantacciyar Doka da zata kawo gyarar yadda ake amfani da Yanar Gizo a Najeriya.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here