Home Lafiya Cibiyoyin kula da lafiya a garuruwanmu duk sun zama kufai -Al’ummar Zamfara

Cibiyoyin kula da lafiya a garuruwanmu duk sun zama kufai -Al’ummar Zamfara

226
0
Zamfara Hospital empty

Najeriya, na ci gaba da kokawa dangane da yadda ayyukan ‘yan bindiga suka sa cibiyoyin kula da lafiya a yankunansu suka koma tamkar kufai sakamakon janyewar ma’aikatan lafiya.

Wasu daga cikin mazauna yankunan sun ce tuni wasu suka shiga aikin sa-kai na cibiyoyin lafiyar domin duba marassa lafiya, yayin da wasu suka kafa ƙungiyoyi don ganin sun samar da magunguna a asibitocin garuruwan nasu.

Mazauna yankunan da suke da wannan matsalar sun ce babban abin da ke damunsu shi ne duk wani jami’in lafiya da za a turo shi garuruwansu ba sa zuwa.

Sun ce saboda yadda ‘yan bindigar ke dauke jami’an lafiyar shi ya sa bas a zuwa ko da an tura su garuruwan.

Wasu kuwa cewa suka yi sun kai shekara biyar a yankunansu bas u da ma’aikatan lafiyar da ke kula da su a cibiyoyin lafiyar.

Sun ce yawanci ‘ya’yansu da suka yi karatun bangaren kula da lafiya ne ke kula da su a garuruwansu.

Mazauna yankunan sun ce a wasu lokutan idan mace za ta haihu sai an yi tafiya mai nisa da ita kafin a samu asibitin za a kula da ita.

Kusan cibiyoyin lafiya 500 ne hukumar kula da lafiya a matakin farko a jihar Zamfarar ta ce ba sa aiki saboda matsalolin tsaro.

Honorabil Kabiru Ahmad Janyau, shi ne shugaban hukumar kula da lafiya a matsakin farko a jihar Zamfara, ya shaida wa BBC irin matakan da suke dauka don kawo karshen wannan matsala.

Ya ce, “Na farko muna kokari mu ga an samu zaman lafiya a wuraren da ke da matsalar tsaro, na biyu kuma a shirye muke muga asibitocin nan da ba sa aiki su dawo su ci gaba da aiki na tsawon sa’oi 24 kamar yadda tsarin kula da lafiya ya tanada.”

Dubban mutane ne ayyukan ‘yan bindiga ya tilastawa barin garuruwansu a wurare daban-daban na jihar Zamfara sakamakon yadda ake dauke mutane don neman kudin fansa.

Jihar Zamfara dai na daya daga cikin jihohin Najeriya da ke fama da matsalolin tsaro. (BBC).

 

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here