Home Noma da Kiwo Gwamnatin Taraiya Ta Ce Za Ta Yi Amfani Da Fasahar Zamani Wajen...

Gwamnatin Taraiya Ta Ce Za Ta Yi Amfani Da Fasahar Zamani Wajen Wadata Kasa Da Abinci

228
0
20231211 150057

Gwamnatin Taraiya ta ce shirye-shirye sun yi  nisa wajen ganin sun fito da Tsare-tsare da  za su tallafawa aikin Noma ta hanyar amfani da fasahar zamani wajen warware matsalolin da suka addabi harkar.

Karamin Ministan Noma, Sabi Abdullahi ne ya sanar da haka jimkadan bayan kammala kare kasafin kudi na shekara ta 2024 a wani zama na hadaka a gaban Majalisar Taraiya jiya Litinin.
Ya ce daga hawan su zuwa yanzu sun lura cewa Najeriya ba ta da wani kundi da ya ke  da bayanai na manoma da ke kasarnan. Sabo da haka sun kuduri niyyar samar da wannan Kundin don samun sauki wajen aikewa da manoman sakonni.
A na sa bangaren Shugaban Kwamiti Noma na Majalisar Datttawa Sanata Salihu Mustapha ya ce Majalisar za ta hada gwiwa da gwamnatin Taraiya wajen ganin an samar da Na’urori na zamani domin sanin manoma da gonakin su ta yin amfani da wata na’ura da a ke kira da GPS.
  1. 20231211 151308
Ya ce hakan zai taimaka wajen samun bayanai cikin sauki. ” Ka na zaune a ofis za ka iya ganin manomi da gonar sa. Idan an raba taki zaka iya sanin cewa ankai takin gona ne ko kasuwa” in ji shi.
Sabo  da haka ya ce Majalisar za tayi duk mai yiwuwa wajen ganin an karawa bangaren Noma kasafin kudi ta yadda za a iya cimma maradun da ake so ayi.
Tun da fari Ministan Noma, Abubakar Kyari ya ce gwamnatin Taraiya ta kuduri niyyar bawa Noma kulawar da ta dace da shi. Inda ya ce hakan ne ya sa Shugaban Kasa Bola Ahmad Tinubu ya kafa dokar tabaci akan harkar Noma.
Kyari ya ce a wannan karon gwamnatin Taraiya za ta kara kasafin kudi fiye da yadda aka saba yi a baya domin shi ne kashin bayan cigaba da samar da zaman lafia.
Shima Shugaban Kwamitin Noma na Majalisar Wakilai, Hon. Bello Ka’ole ya yi wa yan jaridu karin haske akan yadda Majalisar Taraiya ta himmatu wajen ganin an bawa harkar Noma irin kulawar da ta dace da shi.
20231211 171445
Ka’oje ya kara da cewa Majalisar Taraiya ta kuduri aniyar ganin sun yi aika kafada da kafada da gwamnatin Taraiya wajen ganin an samawa Noma kudaden da ya ke bukata.
Ya ce zaman lafia da bunkasar arziki za su samu ne kawai  idan akwai yalwataccen abinci. Sa bo da haka shi ya sa su ka himmatu wajen ganin an bawa Noma kulawar da ta dace.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here