Home Tsaro Boko Haram Ce Ta Kai Hari A Gwoza – Gwamnati

Boko Haram Ce Ta Kai Hari A Gwoza – Gwamnati

44
0
Boko HaramISWAP

Hukumomi a Najeriya sun dora alhakin harin da aka kai garin Gwoza kan mayakan Boko Haram.

A ranar asabar din karshen mako ne wata ‘yar kunar bakin wake ta tashi bam din da ke jikinta lamarin da ya hallaka mutum 18 wasu da dama suka jikkata.

Kwamishinan tsaron cikin gida a jihar Borno, Usman Tar, ya shaida wa BBC cewa kungiyar masu tada kayar baya ta Boko Haram ne suka kai harin, saboda sun san shirin da gwamnati ke yi na maida mazauna kauyuka da garuruwa da ke gudun hijira gidajensu, kuma lamarin bai musu dadi ba.

Gwamnatin jihar Borno dai ta sanar da shirin rufe dukkan sansanin ‘yan gudun hijira da ke jihar daga nan zuwa shekarar 2026. (BBC, AFP).

 

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here