Home Siyasa Majalisar Taraiya Ta Bukaci Da A Gina Gidajen Gyaran Hali Mallakar...

Majalisar Taraiya Ta Bukaci Da A Gina Gidajen Gyaran Hali Mallakar Jihohi

139
0
Hon. Matazu

Majalisar Taraiya ta ce akwai bukatar a gina gidajen Gyaran Hali mallakar Jihohi a wani mataki na banbance su da na Gwamnatin Taraiya lura da irin laifuffuka da ake aikatawa mataki mataki ne.

An gabatar da wannan bukata ne a wani zama na Hadaka tsakanin Majalisar Dattawa da ta Wakilai a lokacin da ake kokarin tantance Kasafin Kudin da ya shafi ma’aikatu da suke karkashin Kwamitin Aiyukan Cikin gida a jiya Laraba.

Dan Majalisar Wakilai mai Wakiltar Musawa da Matazu, da ga Jihar Katsina, Abdullahi Aliyu Ahmed,  kuma Shugaban Kwamitin Aiyuka na Cikin Gida ne ya jaddada wannan bukata a lokacin da ya ke Karin haske ga Yanjaridu a ofishin sa.

Hon. Matazu ya ce Majalisar ta lura cewa akwai kuskure a yadda ake hada masu kananan laifuka da masu manyan laifuffuka a guri guda. In da ya ce hakan ya na haifar da mummunar matsala a kasarnan.

Ya ce ba dadai ba ne a hada wanda ya saci Kaza da wanda ya yi fashi da makami ko kuma dan Boko Haram a wuri guda. Hakan ya ce zai haifar da gagaramar matsala ta yadda mai karamin laifi zai koyi babban laifi ko ma ya ga cewa laifin da ya yi ba ma laifi ba ne. In da idan ya fito maimakon ace ya samu gyara hali sai ya zama babban mai aikata laifi sabo da ya koyi wani abu da ga masu aikata manyan laifuffuka.

Sabo da haka ya ce akwai bukatar a gina gidajen Gyaran Hali mallakar Jihohi ta yadda za a rinka banbance ma su kananan laifi a na ajiye su a Jihohi su kuma masu aikata manyan laifi a rinka ajiye su a Gidajen Gyaran Hali mallakar Gwamnatin Taraiya.

Ga me da yadda za a samar da kudaden da za a aiwartar da wannan aikin, Dan Majalisar ya ce abu ne mai sauki muddin gwamnati ta gamsu cewa akwai bukatar a gina Gidajen domin yin hakan zai taimaka wajen magance matsalar da ake fuskanta ta koyawa masu kananan laifi dabaru na aikata manyan laifuffuka da ake yi a gidajen Gyaran Hali na Gwamnatin Taraiya.

Bayan haka ya kara da cewa a halin yanzu akwai cunkoso a gidajen Gyaran Halin kuma da yawa da ga gidajen sun hade da gidajen jama’a wanda haka matsala ce wadda ba ta kamata ba. In da ya  ce kananan yara bai kamata su rinka ganin masu aikata laifi ba har ma su san irin laifuffukan da su ka aikata.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here