Ranar Ma’aikata: Wanne Hali Ma’aikatan Najeriya Su Ke Ciki?

  74
  0
  IMG 20230620 WA0026

  Yau daya ga watan Mayu, rana ce da akan ware a duk shekara, a matsayin ranar ma’aikata ta duniya. Domin yin waiwaye adon tafiya, game da irin nasarorin da ma’aikata suka samu, da kuma matsaloli ko kalubalan da suke fuskanta a kasashe daban-daban.

  Sai dai ranar ta zo wa ma’aikatan Najeriya daidai lokacin da ƙasar ke fama da matsin tattalin arziki, musamman tun bayan janye tallafin man fetur da gwamnatin Bola Ahmed tinubu ta yi, lamarin da ya janyo zanga-zangar ƙungiyoyin ƙwadago a dukkan sassan ƙasar.

  Ma’aikatan sun koka kan yadda mafi ƙarancin albashi baya iya sayen buhun shinkafa balle sauran buƙatu na yau da kullum. BBC ta tattaro ra’ayoyn wasu daga cikin ma’aikatan, inda wata ma’aikaciya ta ce ” Fatanmu yadda muke farin ciki da wannan rana gwamnati ta duba ta ƙara wa ma’aikata albashi, domin idan aka ƙara masu zai taimaka masu wajen yin rayuwa cikin sauki.”

  Itama wata ma’aikaciyar ta ce suna cikin tsanani na rayuwa, “Musamman mata saboda yawanci a ƙafa muke takawa saboda inda za a kai ka 50 yanzu sai kana da 350, ga tsadar abinci.”

  Ma’aikatan jihar Borno na kan gaba wajen kokawa kan albashin da ake biyansu wanda suka ce bai taka kara ya karya ba.

  Ma’aikatan sun bukaci gwamnatin jihar ta dibi lamarinsu yayin da wasunsu suka ce sun shafe shekaru suna karbar N15,000 a matsayin albashi wasu ma har kasa da N5,000.

  Batun albashin ma’aikatan na jihar Borno dai ya ja hankali a kafofin sada zumunta a Najeriya inda aka dinga yaɗa sakon banki da ke nuna kudi kasa da naira dubu 10 wasu har dubu hudu da wasu ma’aikatan jihar ke karba a matsayin albashi.

  Sai dai gwamnati jihar Borno ta ce ba haka lamarin yake ba, inda ta ce ma’aikatan da basu da ƙwarewa ne ake biya haka wadanda yawancin su ma kamata ya yi gwmanatin ta koresu, amma ta ci gaba da ba su ihsani.

  Duk da cewa gwamnatin jihar ta Borno ta ce ta tausaya wa ma’aikatan ne saboda ba su da ƙwarewa, amma wasu na ganin kudin ya yi kadan lura da yanayin tsadar rayuwa da ake ciki a Najeriya.

  Ƙungiyoyin ƙwadago a Najeriya sun ce suna fafutuka don ganin hukumomi sun amince da sabon mafi ƙarancin albashi, wanda zai dace da halin matsi da tsadar rayuwa da kuma tsananin hauhawar farashin da ake ciki.

  Sun dai gabatar da buƙatar ganin mafi ƙarancin albashin ya kai sama da naira dubu ɗari shida.

  Ƙungiyoyin dai sun sha gudanar da zanga-zangar nuna adawa da matakan da gwamnatin Najeriya ke dauka sai dai za a iya cewa bata sauya zane ba idan aka yi la’akari da halin  da ma’aikatan ƙasar ke ciki. (BBC).

  LEAVE A REPLY

  Please enter your comment!
  Please enter your name here