Home Zirga zirga Kasafin Kudin 2024: Majalisar Dattawa Ta Nu Na Takaicin Ta Na Kudaden...

Kasafin Kudin 2024: Majalisar Dattawa Ta Nu Na Takaicin Ta Na Kudaden Da A Ka Warewa Hukumar FERMA

150
0
Sen. Hussaini

Majalisar Dattawa ta nu na takaicin ta akan yadda aka gabatar ma ta da Kudade da aka shirya kashewa a cikin Kasafin Kudi na shekara ta 2024 domin gyaran tituna na Gwamnatin Taraiya da ke Kasarnan.

Shugaban Kwamitin FERMA na Majalisar Dattawam, Sanata Babangida Hussaini ne ya baiyana wannan takaici jimkadan bayan kammala wani zama na Hadaka da aka gudanar tsakanin Majalisar Wakilai da ta Dattawa a ya yin gabatar da Kasafin Kudi na Ma’aikatar Aiyuka da ya gudana a yau Talata.

Ya ce naira bilyan 50 da aka warewa FERMA ya nu na karara cewa ba da gaske a ke yi ba wajen ganin an gyara titunan Kasarnan wadan da su ke cikin mummunan yanayi.

Ya kara da cewa titunan masu nisan zango 26,000 mallakar Gwamnatin Taraiya wadan da a ka yi wa kima na naira Tiriliyan 18 abun kunya ne a ce an ware naira biliyan 50 kacal don kula da wadannan tituna.

Sanata Hussaini ya ce kyawawan tituna su na daga darajar Kasa; wanda hakan ya kan kawo yalwatar arziki domin zai bawa yankasuwa da masu zuba jari su zaga kasar cikin kwanciyar hankali don bunkasa tattalin arzikin Kasar ba tare da wata wahala ba.

Sabo da haka ya ce, Majalisar Taraiya za ta hada gwiwa da Ma’aikatar Aiyuka wajen ganin an Karawa Hukumar FERMA kaso mai tsoka a wannan Kasafin Kudin don inganta tsaro da tattalin arziki na Yan Najeriya.

A wani bangare kuma, ya karyata jita-jita da ta ke zagayawa cewa a na nuna fifiko wajen ware Kudade don gudanar da manyan aiyuka musamman tituna ga wani yanki. In da ya kara haske da cewa, gina titi mai nisan zango 10 a Jihar Sokoto dai-dai ya ke da gina titi mai nisan zango daya a Jihar Rivers sabo da bambanci na yanayin Kasar wuraren.

Sanatan ya yi kira ga Yan Najeriya da su bawa Majalisar Taraiya da Gwamnatin Taraiya goyon baya wajen kula da titunan Kasarnan domin idan an yi haka zai karawa titunan inganci wanda zai sa su dade ba su lalace ba ta yadda hakan zai tallafawa kasuwanci da bunkarsar tattalin arzikin Kasarnan.

Da ga karshe Sanata Hussaini ya ce Majalisar Taraiya ta sha alwashin hada gwiwa da Gwamnatin Taraiya wajen ganin an samawa Yan Najeriya ingantattun tituna wadanda za su taimaka wajen cika burin Shugaban Kasa Bola Ahmed Tinubu na samar da sabuwar Najeriya da kowa zai yi alfahari da ita.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here