Home Tsaro Barazanar Tsaro: Majalisar Dattawa Ta Umarci Rundunonin Tsaro Da Su Bincika Mamamlaka...

Barazanar Tsaro: Majalisar Dattawa Ta Umarci Rundunonin Tsaro Da Su Bincika Mamamlaka Guraben Hakar Ma’adanai A Kasarnan

148
0
Sen. Sani Musa

Majalisar Dattawa to umarci rundunonin tsaro da ke kasarnan da su yi bincike akan mamallaka na guraren da ake hakar ma’adanai da ke kasarnan a wani mataki na gano masababin barazanar tsaro da ta addabi kasarnan.

Umarnin ya biyo bayan wani Kuduri da Dan Majalisar Mai Wakiltar Jihar Niger ta … Sanata Sani Musa ya gabatar ranar Talata sakamakon barazanar tsaro da ta addabi Jihar ta sa.

Ya ce lamarin tsaro ya ta’azara a Jihar ta sa ta Nija in da ya ce kusan kullum sai an kama mutane domin neman kudin fansa a wani lokaci ma akan kashe mutane tare da yin awun gaba da daruruwan shanun su.

“abun akwai takaici yadda ake kwasar mutane domin karbar kudin fansa. Wani lokaci kuma a kwashe daruruwan shanu a tafi da su. Ba gaskiya ba ne ace an kwashi shanu dari biyar a tafi da su a cikin kasarnan amma a ce wai ba’a san wadanda su ka kwashi shanun ba”.

Sanata Sani Musa ya ce sabo da haka ne Majalisa ta umarci rundunonin tsaro da su gaggauta yin bincike domin a gano mamamlaka gurare da ake hakar ma’adanai domin akwai alaka tsakanin hakar ma’adanai da satar mutane da ake yi.

“abun lura anan shine a daji ake hakar ma’adanai amma wadanda suke hakar ma’adanai suna aikin su ba wata tsangwama amma talakawa da ke zagaye da gurare da ake hakar ma’adanai kullum ana kashe su kuma ana kama wasu domin neman kudin fansa. Wannan ya nuna karara cewa da walakin goro a miya.”

Bayan haka Sanatan ya ce, da yawa da ga cikin wadanda suke zuwa domi hakar ma’adanai ba Yan Kasarnan bane ana kawo su ne da ga Chadi da Nijar da Kamaru da ga Gabon kai harma da Yan China. Kuma suna ibar ma’adanai yadda suke so su yi tafiyar su sabo da su na bawa hakimai da dagadai da ke wuraren da ake hakar ma’adanan dan wani abu kalilan da bai taka kara ya karya ba.

Sanata Musa ya ce Majalisa Taraiya ba za ta zuba ido ta ga ana zaluntar kasarnan da Yan kasarnan amma ta yi shiru ba sabo da haka ne ta umarci jami’an tsaro da su yi duk binciken da ya kamata domin kawo karshen wannan matsala.

Sanatan ya ce Majalisar ta amince da samar da wani kundi da ke dauke da sunaye da hotuna na duk wadanda suke hakar ma’adanai a kasarnan manyan su da kananan su ba tare da la’akari da zurfin ilimin su ba.

Da ga karshe Majalisar ta bukaci da a samar da wata runduna ta musamman a yankin na Nija domin su saka ido akan abubuwan da su ke faruwa a yankin tare da daukar matakai da suka da ce domin kawo karshen barazanar tsaro da ta addabi kasarnan.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here