Home Siyasa Majalisar Dattawa Ta Sha Alwashin Ladabtar Da Duk Jami’in Gwamnatin Da Ya...

Majalisar Dattawa Ta Sha Alwashin Ladabtar Da Duk Jami’in Gwamnatin Da Ya Ki Amsa Kiranta

856
0
Sen. Kaka

Majalisar Dattawa ta sha alwashin ganin cewa ta dauki mataki na ladabtarwa akan duk wanda ya yi kokarin ya kawo cikas wajen ganin yan Najeriya sun amfana kamar yadda ya kamata dag a dukkan tallafi da gwamnatin taraiya ta bayar ko ta kuduri niyyar bayarwa.

Shugaban Kwamitin na Musamman na Majalisar Dattawa, Sanata Kaka Shehu ne ya sanar da haka a wajen kaddamar da Kwamitin wanda ya gudana a Majalisar a yau Laraba.

Sanata Kaka y ace Majalisa ta goma ta sha bambam da sauran Majalisu da suka shude domin akwai yarjejeniya tsakanin  Fadar Shugaban Kasa da Majalisar na cewa za su hada hannu da karfe wajen ganin anyi auyuka da za su inganta rayuwar Yan Najeriya ba tare da la’akari da bambancin yare ko kabila ba.

Sanatan ya kara da cewa Majalisar ba zata yarda da cin kashi ba da ga duk wani jami’in gwamnati da Majalisar ta gaiyata gabatan domin ya bata bahasi na aiyukan da suka shafi ma’aikatar sa.

Y ace akwai yarjejeniya tsakanin Majalisar da Shugaban Kasa na cewa za’a ladabtar da duk wani Jami’in gwamnati day a ki amsa kiran Majalisar ko kuma ya nemi day a raina ta.

Sanata Kaka y ace Kwamitinsa ya shirya tsaf domin ya yi duk abun day a kamata wajen ganin Yan gudun hijira da masu bukatar agaji sun sami kulawar da ta dace a ko ina suke a Najeriya harma da kasashe da suke wajen Najeriya kamar su Nijar da Kamaru da Chadi da sauran kasashen Duniya.

Har ila yau, Sanatan y ace Kwamitin nasa zai tabbatar ya yi  bibiya da sa’ido akan duk wani tallafi da gwamnatin Taraiya ta tsara wajen ganin cewa wadanda aka shirya tallafin domin su sun amfana kai tsaye.

Y ace Kwamitin zai tabbatar da cewa wadanda aka shirya tsari domin su sune suka amfana ta hanyar fito da tsare tsare da za su kawas da son zuciya da almundahana da babakere da wasu keyi a baya.

A wani bangaren kuma Sanata Kaka Shehu ya yi alkawarin ganin cewa mutanen da suka turo shi Majalisar Taraiya sun sami wakilci na gari ta hanyar gabatar da kudure kudure da zasu inganta rayuwar su.

Har ila yau, ya fito da shirye shirye na tallafawa Jama’ar sa a fannoni da dama kamar harkar Ilimi da Noma  da lafiya. Wadanda ya ya ce zai gudanar das u cikin tsari ta yadda duk wadanda aka shirya shirin domin su sun amfana.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here