Home Diplomasiyya Shugabannin Saudiyya da Iran karon farko sun tattauna a kan rikicin Gaza

Shugabannin Saudiyya da Iran karon farko sun tattauna a kan rikicin Gaza

227
0
saudia and Iran

Kafofin yada labaran Iran da Saudiyya sun ce shugabannin kasashen biyu sun tattauna batun rikicin Isra’ila da Falasdinawa, a wata tattaunawa ta farko ta wayar tarho tun bayan da suka dawo da huldar diflomasiyya a tsakaninsu.

Sun ce Shugaba Ebrahim Raisi da Yarima mai jiran gado na Saudiyya Mohammed bin Salman sun yi magana kan bukatar kawo karshen abin da ya bayyana a matsayin laifukan yaki a Gaza da Israil ke aikatawa.

Kamfanin dillancin labaran Saudiyya ya ce Riyadh ta jaddada yunkurin goyon bayanta ga Falasdinawa, da kuma bukatar a shawo kan lamarin ta diflomasiayya.

Majalisar Dinkin Duniya ta ce mutune 340,000 ne aka tilastawa barin muhallinsu, yayin da Isra’ila ke ci gaba da kai hare-haren martani ga harin da Hamas ta kai ranar Asabar.

Isra’ila ta hana mutane fita ta ko ina, duk da cewa wasu sun yi nasarar tsallakewa daga yankin.

Isra’ila ta katse wutar lantarki da ruwan sha a Gaza.

Sai dai kuma, ƙasashe da ƙungiyoyi na ci gaba da kiran a samar da yanayin kai tallafi Gaza da kuma bai wa ƴan gudun hijira damar ficewa.

Hukumomi a Masar sun ce an fara tattaunawa don ganin an ƙulla yarjejeniyar kai ɗauki ga mutanen da yaƙin ya ritsa da su.

Amurka ma ta ce tana tattaunawa da Isra’ila a kan yadda za ta taimaka wajen kwashe fararen hula daga Gaza, bayan shafe kwana biyar Isra’ilan tana luguden wuta.

Sakatare-janar na Majalisar Dinkin Duniya, Antonio Guterres, ya ce dole ne a bayar da damar shiga da muhimman kayan buƙata ga mutanen da ke Gaza.

Scott Paul na ƙungiyar agaji ta Oxfam ya ce abubuwan da ke faruwa a Gaza ba su da daɗin ji.

Ya ce ‘’fatan mu shi ne masu faɗa a ji, a duniya za su saurari muryoyin mutanen da lamarin ya ritsa da su, su kuma dubi hotunan da suka bayyana na irin wahalar da ake ciki. Yanzu haka yanke lantarki da ruwa da aka yi daga yankin ya shafi duk wanda ke zaune a Gaza. Mutane fiye d miliyan ɗaya ne ke buƙatar abinci… wannan ba labari mai kyau bane’’.

A ɓangare guda kuma rahotanni na cewa dakarun Isra’ila na ci gaba da matsawa kusa da Gaza, a wani ƙoƙari na afkawa ciki ta ƙasa, bayan hare-haren sama.

Blinken na kan hanyar sauka a Isra’ila

Sakataren harkokin wajen Amurka zai isa Isra’ila nan da sa’o’i kaɗan.

Ba aikin shiga tsakani zai je ba domin kawo ƙarshen wannan rikici: kuma bai yi kira a tsagaita wuta ba.

Sakonsa shi ne Isra’ila ta sani tana da goyon bayan Amurka – yau da gobe da kuma ko da yaushe.

Shi da Shugaba Biden sun tattauna kan munin harin da Hamas ta ƙaddamar: Sun ce dole Isra’ila ta ɗauki matakin kare kanta, ta kuma kawo ƙarshen wannan barazanar da take fuskanta, ta kuma tabbatar ta yi wa tufkar hanci ta yadda ba za ta iya faruwa ba a nan gaba.

Sun nemi Isra’ila ta bi dokokin yaƙi na duniya, ta gujewa cutar da fararen hula, amma a bayyane take cewa suna so tare da goyon bayan ta yi amfani da dukkan ƙarfinta domin murƙushe Hamas.

Amerikawan suna tattauna da Masar da kuma Isra’ila kan yadda fararen hula za su samu hanyar ficewa daga Gaza, amma lamarin cike yake da sarƙaƙiya in ji Blinken.

Adadin wadanda suka mutu ya karu

Shugaba Ebrahim Raisi da Yarima Bin Salman sun tattauna kan “buƙatar kawo ƙarshen laifukan yaƙi kan Falasɗinawa,” kamar yadda jaridun Iran suka ruwaito.

Yariman na Saudiyya, ya “tabbatar da cewa Masarautar na yin iya ƙoƙarinta wajen tattaunawa da ƙasashen duniya da na yankin domin daƙile wannan yaƙi da ke ruruwa,” kamar yadda kamfanin dillancin labarai na Saudiyya ya ambato.

Kamfanin ya ruwaito Yariman ya jaddada cewa Saudiyya na watsi da duk wani shiri na kai hari kan fararen hula a ko ina.

Ma’aikatar Lafiya ta Falasdinu ta ce mutum 1,200 ne suka mutu tun lokacin da Isra’ila ta fara kai hare-harenta ta sama, a matsayin ramuwa kan harin da Hamas ta kai mata a safiyar ranar Asabar.

Mutuwar da aka samu a duka ɓangarorin biyu ta kusa kai wa 2,500.

Tun da fari, ma’aikatar harkokin tsaron Isra’ila ta ce an kashe Isra’ilawa 1,200 a harin Hamas na ƙarshen mako sai dai ana tsammanin adadin zai iya zarce haka.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here