Home Uncategorized Zanga-Zangar Nuna Goyon-Bayan Falasdinawa Ta Karade Manyan Biranen Burtaniya

Zanga-Zangar Nuna Goyon-Bayan Falasdinawa Ta Karade Manyan Biranen Burtaniya

148
0
Protest in Britain OVER Gaza

Masu zanga-zangar nuna goyon-bayan Falasdinawa sun karade manyan birane Landan domin neman duniya tayi adalci kan luguden wutar da ake yi a Gaza.

Dubban mutane a sassan daban-daban na duniya na ci gaba da fantsama kan tittuna domin zanga-zanga da bayyana takaicinsu kan rikicin da ake tafkawa tsakanin Falasdinawa da Isra’ila na sama da mako guda.

Dubban mutane sun fito suna zanga-zangar a birnin Landan, wadda ta kai su har kofar gidan firaministan Burtaniya Rishi Sunak. Masu gangamin na nuna bakin cikinsu kan munanan hare-haren da suka ce sojojin Isra’ila na kai wa kan fararen hula a yankin Zirin Gaza.

Wadannan masu zanga-zanga a birnin Landan ba wai asalin Falasdinawa ba ne kadai, akwai musulmai daga kasashe daban-daban mazaunan wannan kasa, da ke nuna goyon-baya da takaicin kisan da ake yi wa Falasdinawa fararen hula.

Masu zanga-zangar dai na zargin Burtaniya da kawayenta da nuna goyon baya ga Isra’ila a fadan da aka kwashe fiye da mako daya ana gwabazawa.

Ahmad Ghassan na daya daga cikin masu zanga-zangar. Ya ce “Ba za mu kira abin da ke faruwa da sunan rikici ba, sai dai muna son duniya ta san cewa, kokari ne na karbe abin da tun asali namu ne, duk da cewa kasashen duniya da dama har da manyan kafafen yada labarai na sukar Falasdinu har nan Brutaniya, Firaiminista Rishi Sunak bai ce uffan kan halin da Falasdinu ke ciki ba, to shi ya sa mu muka zabi mu fito mu sanar wa duniya cewa, a shirye muke mu yi wannan fafutukar kwatarwa kanmu ‘yanci ba tare da mun bata lokaci ba’’

Aman Ayoub dan kasar Bangladesh ne, da ke da ra’ayin cewa, tura ce ta kai bango, saboda haka bai wa Falasdinu ‘yancin zama kasa mai cin gashin kanta ne kawai mafita a wannan tashin hankalin.

”Na shiga wannan zanga-zangar ta lumana domin jan hankalin duniya domin a dakatar da fadan da ake yi tsakanin Isra’ila da Falasdinu, ana ta kashe mutanen da ba su ji ba-ba su gani ba, ana gallazawa mutane azaba da jefa rayuwarsu cikin ukuba, laifi dadai da kisan kiyashi ake aikatawa, don haka muka fito muna neman a kawo karshen rikicin tare da bai wa Falasdinu ‘yancin zama kasa mai cin gashin kanta’’

A gefe guda kuma, suma wasu Yahudawan Isra’ila sun yi tasu zanga-zangar lumanan a yammacin jiya Lahadi a kusa da ginin majalisar Burtaniya domin nuna takaici da neman sakin wasu mutane da suka ce ana garkame da su sakamakon wannan rikici.

Isra’ila na ci gaba da nanata cewa ba zata raga a wannan yaki ba, har sai ta ga bayan Hamas duk da yanayi na muni da ake ciki a Gaza.

Shin ko akwai sauran damar komawa kan teburin sulhu? Adam Moukhtar Imam wani mai bibiyar siyasar Gabas ta Tsakiya da ke birnin Alkhahiran Masar ya ce shakka babu abu ne mai yiyuwa.

Kawo yanzu dai rayuka fiye da dubu biyu suka salwanta a sakamakon wannan rikici a yayin da Isra’ila ke cewa za ta ci gaba da kai hare-hare babu kakkautawa a yankin Zirrin Gaza.

Shugaban Amurka Joe Biden ya fito ya yi kira ga Isra’ila kan tayi takatsantsan. Sannan Majalisar Dinkin Duniya na ci gaba da nuna damuwarta kan mawuyacin hali da bukatar agaji da ake fuskanta a Gaza. (Muryar Amurka).

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here