Home Uncategorized Rashin Lafiya Ne Ya Hana Sadiya Faruq Amsa Gaiyata – EFCC

Rashin Lafiya Ne Ya Hana Sadiya Faruq Amsa Gaiyata – EFCC

219
0
IMG 20240104 WA0028

Wata majiya daga hukumar EFCC mai yaƙi da yi wa arzikin Najeriya zagon ƙasa ta shaida wa BBC dalilin da ya sa tsohuwar ministar jin ƙai, Sadiya Umar Farouq ba ta amsa gayyatar hukumar ba.

A cewar majiyar, tsohuwar ministar, wadda ake zargin ta da hannu a badaƙalar halasta kuɗin haram naira biliyan 37.1 ta nemi EFCC ta ƙara mata lokaci saboda dalilai na rashin lafiya.

Tun farko, kafofin yaɗa labaran Najeriya sun ruwaito cewa tsohuwar ministar ba ta bayyana a hedikwatar hukumar ta EFCC ba.

A farkon makon jiya ne, Sadiya Umar Farouq ta fitar da wata sanarwa, wadda a ciki ta musanta hannu a badaƙalar da ake zargi. Ta ma yi iƙirarin cewa kwata-kwata ma ba ta san ɗan kwangilar da rahotanni ke cewa hukumar EFCC ta kama a binciken da take yi dangane da batun ba.

Wata majiya daga EFCC a ranar Laraba ta tabbatarwa da BBC cewa hukumar na sa ran isar tsohuwar ministar ta zamanin Shugaba Muhammadu Buhari, zuwa ofishinsu da ke Abuja.

Sai dai jaridar Punch ta ruwaito cewa jami’an EFCC sun shafe tsawon sa’o’i suna dakon isar Sadiya Farouq, amma har lokaci ya ƙure ba su ga tsohuwar ministar ba, kuma ba tare da samun wani bayani daga gare ta a kan dalilinta na gaza bayyana a hukumar ba.

EFCC dai ta gayyace ta ne tun a makon jiya domin ta yi ƙarin haske game da zargin halasta kuɗin haram a ƙarƙashin shugabancinta.

A saƙon da ta wallafa a shafinta na X, tsohuwar ministar ta ce “Akwai rahotanni da dama da ke alaƙanta ni da wani bincike na hukumar EFCC game da ayyukan wani james Okwete, kwata-kwata ma ni ban san shi ba.”.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here