Home Kwadago Dalilan Bankin CBN Na Korar Mutum 117 A Kasa Da Kwana 20

Dalilan Bankin CBN Na Korar Mutum 117 A Kasa Da Kwana 20

151
0
IMG 20240301 WA0028

Babban bankin Najeriya CBN ya kori ma’aikata sama da 117 a cikin abin da bai gaza kwana 20 ba.

BBC ta gano lamarin ya fi shafar manyan ma’aikata masu matsayin darekta da mataimakansa a sassan bankin guda uku da suka hada da sashen da ke kula da tallafi da mai kula da kwantaragi da kuma mai kula da lafiya da magunguna.

Yanzu mafi yawan ma’aikatan bankin cikinsu ya ɗuri ruwa saboda rashin sanin mai gobe za ta haifar.

Wata majiya daga bankin dai ta shaida wa BBC cewa korar yanzu aka fara domin “ba ma a zo sashen da ke kula da hada-hadar kudaden musaya ba.”

Babu dai wanda ya yarda BBC ta naɗi muryarsa kan lamari, wasu na cewa ko hukumomin bankin ba za su iya cewa komai ba saboda rashin sanin inda aka dosa.

CBN na ci gaba da bincike kan badaƙalar da aka tafka tun daga wasu shekaru da suka wuce baya.

Sai dai wasu na ganin “abin da bankin yake yi abu ne mai kyau domin an tafka badakala a bankin. To amma a wadanda aka kora din akwai kalilan da watakila su victims ne wato ba su san hawa ba ba su san sauka ba. Saboda haka ya kamata a yi bincike sosai”, in ji majiyar tamu a CBN.

A baya-bayan nan ne dai bankin ya sanar cewa har yanzu ‘yan Najeriya ba su biya bashin da suka karba ba na tallafin Korona, inda bankin ke neman a mayar masa da fiye da naira biliyan 250.

Wannan na zuwa a daidai lokacin da tsohon gwamnan bankin, Godwin Emefele ke fuskantar shari’a bisa tuhume-tuhumen rashawa da cin hanci.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here