Home Siyasa Abba Gida-gida ya shawarci masu bai wa gwamnatin Kano bashi su dakata

Abba Gida-gida ya shawarci masu bai wa gwamnatin Kano bashi su dakata

192
0

Zaɓaɓɓen gwamnan Kano, Injiniya Abba Kabir Yusuf ya shawarci masu bai wa gwamnatin jihar bashi a wannan lokaci, su dakata.

A wata sanarwa da sakataren yaɗa labaransa, Sunusi Bature Dawakin Tofa ya fitar, gwamnan mai jiran gado ya shawarci masu ba da bashi na cikin gida da na ƙetare ga gwamnatin Kano mai barin gado, su dakatar da hakan daga 18 ga watan Maris zuwa 29 ga watan Mayu.

Sanarwar ta ci gaba da cewa sabuwar gwamnatin ba za ta yi la’akari da bashin da jihar ta karɓa ba, matuƙar ba a sanar da ita game da hakan ba.

Ta kuma ce masu bin gwamnatin jihar bashi, su kwan da sanin cewa za a sake nazarin ƙa’idojin bashin da suka bai wa gwamnati mai barin gado, bayan kammala bincike a kan duk bashin da ake bin Kano.

A tsakiyar wannan mako ma, zaɓaɓɓen gwamnan ya fitar da irin wannan sanarwa da ya ce shawara ce ga masu gine-gine a filayen gwamantin jihar, inda ya nemi su dakata.

Sai dai, washe gari da fitar da shawarar, gwamnan Kano mai barin gado, Abdullahi Umar Ganduje ya mayar da martani, yana cewa ya kamata gwamnan mai jiran gado ya yi haƙuri, ya daina fitar da sanarwar hukuma da sunan shawara.

A sanarwar da ya fitar, kwamishinan yaɗa labaran jihar, Muhammad Garba ya ce abin da zaɓaɓɓen gwamnan ya yi, tamkar ba da umarni ne a kan wani batu da ya shafi manufar gwamnati, a daidai lokacin da gwamna mai ci har yanzu ke da cikakken iko.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here