Home Tsaro Ba Ma Goyon Bayan Kafa Yansandan Jihohi A Najeriya Inji Shugaban Yan...

Ba Ma Goyon Bayan Kafa Yansandan Jihohi A Najeriya Inji Shugaban Yan Vigilante na Kasa – Kaftin Bakori

196
0
IMG 20240326 WA0024
Shugaban Kungiyar Yan Sakai da aka fi sani da Vigilante Group of Nigeria,  Kwamanda Janar na Kasa, Nebi Kaftin, Umar Bakori ya ce ba sa goyon bayan kafa Yansandan Jihohi A Najeriya.
Shugaban ya sanar da rashin amincewar ta su ne bayan da Kungiyart a gabatar da gyare-gyare da ta ke so a yi a cikin Kundin Tsarin Mulki ga Majalisar Wakilai a yau Talata.
Kaftin Bakori ya ce wannan yunkuri na kafa Yansandan Jihohi wata hanyace da ake amfani da ita wajen cinhanci da rashawa ta hanyar kwasar makudan kudade da sunan samar da tsaro.
Bakori ya ce Gwamnatin Taraiya ta kashe sama da Naira biliyan 13 don samar da Yansandan Al’umma amma hakan ya wuce babu wani canji da aka samu.
Ya bayar da misali da ikirarin Gwanonin Jihohin Katsina da Zamfara na cewa sun kashe naira biliyan 10 da 17 domin samar da tsaro a jihohin na su amma hakan ya kasa samar da tsaron da a ke bukata.
Ya ce Gwamnatin Jihar Ekiti ta kashe naira biliyan 1.4 da Jihar Ondo sun kashe naira biliyan 2 amma ba wata nasara.
In da ya ce a maimKon ha ka kamata ya yi gwamnonin su su tallafawa Kungiyar Vigilante don samar da tsaro a jihohin na su. Yayin da ya kara da cewa tuni Vigilante ta na da mambobi sama da miliyan daya a Najeriya.
Kaftin Bakori ya ce mambobin su na da masaniya na wuraren da suke aiki kuma yan asalin yankin ne, sabo da haka suna da masaniya na lungu da sako na inda ma su laifi su ke. Sabo da haka suna taimakawa jami’an tsaro da bayanai.
Ya ce Kungiyar ta su tana bukatar gwamnati ta basu kulawar da ta kamata ta hanyar basu tallafi na kudade da kulawar data kamata a wani mataki na karfafa mu su gwiwa na cigaba da yin abun da suka sa kansu sama da shekaru 30 da suka gabata.
Shugaban ya bukaci Gwamnati da samar da wata cibiya da za ta rinka bawa Yan Vigilante horo da Tsare-tsare da Dokoki don kyautata aikin su ta re da samar musu da kayan aiki da zai taimaka wajen samun nasarar aikin da su ke yi.
Kwamandan ya nuna jin dadinsu na yadda Sojoji su ke basu hadin kai da goyon bayan ta yin aiki tare. Wanda hakan ya haifar da nasarori wajen kubutar da Yan makarantar da aka yi garkuwa da su a Kuriga da Chibock da sauran su.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here