Home Uncategorized Majalisar Dattawa Ta Umarci Kamfanin TCN Da Ya Gaggauta Gyara Wutar Lantarkin...

Majalisar Dattawa Ta Umarci Kamfanin TCN Da Ya Gaggauta Gyara Wutar Lantarkin Yankin Arewa Maso Gabas

179
0
20240214 152241

An umarci Kamfanin Rarraba Wutar Lantarki na Kasa ya dauki matakin gaggawa na mayar da wutar Lantarki da aka lalata a Yankin Arewa maso Gabas domin dawo da al’amuran rayuwa su dawo kamar yadda ya kamata.

Sanata Anthony Siyako Yaro mai wakiltar k7dancin Jihar Gombe ne ya gabatar da wannan bukata ta gaggawa wajen ganin cewa mutanen yankin sun shafe tsawan.lokaco babu wutar lantarki wanda haka ya jefa mutanen yankin cikin mawuyacin hali.

Sanata Yaro ya kara da cewa wutar lantar ta shafi rayuwar mutane ta fannoni da dama kamar aiwatar da aiyukan yau da kullum kamar nika abubuwan da ake bukata wajen abinci da sana’o’I irin su markade da dinki da samar da ruwan sanyi da lemo .musamman ma samar da ruwan sha ga Alumma wanda shine ginshikin rayuwa da sauran muhimman bukatun da sai da wutar lantarkin

Y ace a takaice rayuwa bazata yi dadi ba idan babu wutar lantarki shi ya sa Sanatoci Yankin Arewa maso Gabas suka hadu suka gabatar da Kuduri na gaggawa a gaban Majalisar Dattawa domin su hanzarta gyara wutar lantarki da aka lalata a yankin.

Sanatan ya ce koda yake Kamfanin TCN ya yi alkawarin gyara wutar lantarkin cikin kwanaki uku amma akwai bukatar ganin cewa sun hanzarta gyara wutar cikin kankanin lokaci domin dawo da al’amuran rayuwa so sai yadda ya kamata a yankin.

Bayan hakan, Sanatan y ace akwai bukatar Kamfanin na TCN ya dauki matakai na ganin ba’a sake barnata kayayyakin wutar Lantarki a yankin bat a hanyar daukar matakai na kariya kamar yadda ake kare bututun Man Fetur a Kasarnan.

Ana su bangaren ya ce Sanatocin Yanki sun dauki alkawarin taimakawa yunkurin Kanmfanin TCN da jami’an Tsaro na sa Kai domin su tabbatar hakan bata sake faruwa ba. Sai dai yace wasu wayoyin wutar Lantarki suna cikin daji ne sabo da haka akwai bukatar a samar da na’urori na zamani da za su taimaka wajen sanar da kamfanin a duk. Lokacin da aka sami matsala

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here