Home Tsaro 2011-2019 ‘Yan bindigar Zamfara: Sun yi Garkuwa da Mutum 3,672, an Biya...

2011-2019 ‘Yan bindigar Zamfara: Sun yi Garkuwa da Mutum 3,672, an Biya Fansar Naira Biliyan 3

231
0

Rahoton da Gwamnatin Jihar Zamfara ta fitar ya nuna cewa tsakanin watan Yuni 2011 zuwa Mayu 2019, ‘yan bindigar Jihar Zamfara sun karɓi sama da naira bilyan 3 kuɗin fansar mutanen da su ka riƙa yin garkuwa da su.

Haka kuma rahoton ya tabbatar cewa fiye da mutum 190,340 ne su ka rasa muhallin su sanadiyyar hare-haren ‘yan bindiga.

Rahoton wanda Kwamitin Bincike wanda Gwamna Bello Matawalle ya kafa cikin 2019 ya kafa ƙarƙashin shugabancin tsohon Sufeto Janar na ‘Yan Sandan Najeriya, Mohammed Abubakar, ya nuna cewa waɗannan shekaru takwas cikin mulkin tsohon Gwamnan Zamfara Abdul’aziz Yari, mata 4,983 sun zama ‘yan takaba, bayan kisan mazajen su da ‘yan bindiga su ka yi.

Sannan kuma ‘yan bindiga sun maida ƙananan yara har 25,050 sun zama marayu bayan kisan iyayen su da aka yi.

Rahoton kamar yadda Kakakin Yaɗa Labaran Gwamna Matawalle, Sulaiman Zailani ya fitar, ya ce a shekarun takwas an sace shanun makiyaya Fulani guda 2,015, awaki da tumaki 141, jakai da raƙuma.

Wannan rahoto ya ƙara da cewa an lalata motoci da babura 147,800, waɗanda ko dai aka lalata ko kuma aka ƙone ƙurmus.

Yanzu Kashe-kashen Ya Ragu -Gwamnatin Zamfara:

Yayin da ake ci gaba da kashe mutane ana garkuwa da su tare da ƙaƙaba masu haraji a wasu yankunan jihar, har da hana manoma zuwa gona da cin kasuwanni, Gwamnatin Jihar Zamfara ta ce kashe-kashe ya ragu a jihar da kuma garkuwa da mutane.

Sannan kuma ba a san yawan mutanen da aka kashe ko aka yi garkuwa da su ba a zamanin wannan gwamnatin ta Bello Matawalle.

Jaridar Premium Times tace, wannan rahoto dai bai bayyana adadin mutanen da aka kashe a waɗannan shekaru takwas ba. Kuma ba ya ɗauke da adadin ɓarnar da aka tafka daga Yuni 2019 zuwa Agusta 2022 zamanin mulkin Gwamna Bello Matawalle.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here