Home Muhalli Ambaliyar Ruwa a Kano : Laifin Wanene?

Ambaliyar Ruwa a Kano : Laifin Wanene?

163
0

Daga: Hussaini Umar Najiddah

Rabon da Kano taga ambaliyar ruwan irin wanda akayi ranar Litinin, masana sun ce tun shekarar ta 1988; inda daruruwan gidaje da kokiyoyi suka salwanta, bugu da kari da asarar rayuwa masu yawan gaske.

Hakika wannan shekarar ta 2022 ita ma ta zo mana da irin wancan kalubalen, ko da ya ke bai kai wancan ba. Sai dai wannan karon dubban miliyoyin kudade aka rasa. Abun nufi shi ne kayayyakin ‘yan kasuwa na dubban miliyoyi sun salwanta a dalilin wannan ambaliyar ruwa.

A ‘yan kwanakin nan jaridar Viewfinder ta ziyarci kasuwar             Kantin Kwari da kasuwar Kurmi da unguwar Fagge layin bola inda mu ka ganewa idanun mu irin barnar da ruwan saman ya yi.

Kasuwar Kantin kwari wata kasuwa wacce tayi fice akan sayar da yadiddika a Najeriya. ‘Yan kasuwa kanana zuwa manyan su sun yi asarar kayayyakin su wanda a takaice takai ta Naira miliyan Dubu daya kamar yadda mai magana da yawun Kungiyar ‘Yankasuwar kantin Kwari Mallam Hamisu Dandago ya shaida mana.

Ya kara da cewa hakika gine gine da aka yi a kasuwar da toshewar magudanan ruwa su ne ummul aba’isin na wannan ambaliyar ruwan.

Su ma da muka ji ta bakin su ‘yan kasuwar da suka yi asara sun bayyana mana cewa hakika ruwa ya yi musu barna ta yadda kayayyakin su na yadiddika suka jike da ruwa inda wadan su da yawan su ma sun rasa kayan su sabo da sun lalace. Kamar yadda Mallam Kabiru ya sahida mana.

Malam Kabiru ya ci gaba da cewa shi kansa ya rasa kaya na Naira Miliyan daya da dubu dari uku.

To, abin tambaya anan shine laifin wanene? Kamar yadda wani dan-kasuwa ya shaida wa jaridar viewfinder wanda ya bukaci da mu sakaya sunansa yace, duk wadannan abubuwa da suke faruwa laifin Yan kasuwa ne.

Saboda su ne suke sayen hanyoyi a cikin kasuwanni don su kara gina rumfunan su. Ya kara da cewa wadannan gine gine da ake yi ba ji ba gani sune suka jawo ambaliyar ruwa a kasuwar.

Y ace, duk sun matse hanyoyin da ya kamata ruwan ya bi. Sannan har ila yau ya karawa da cewa magudanan ruwan da suke kasuwar kwari duk ‘yan kasuwa sun cike su da shara da kasar da suke sharewa da ga hanyoyin kasuwar.

Har ila yau, wasu ‘yan kasuwar sun lika laifin ga ‘yan siyasa kwadayayyu da suke zuwa su nemi gwamnati ta basu gurare da aka ware don hanya, kamar yadda mu ka ga gine gine da yawa a Kantin kwarin ciki har da layin nan da ake masa lakabi da Layin Ta’ambu.

Bayan maganar kantin kwari, unguwar Fagge ma ba a barta a baya ba. Kowa ya san wannan babbar kwatar da ta biyo ta bayan Filaza wacce tayi arewa da kasuwar kwari wato tabi ta titin IBB in da zai kai mutum kasuwara Abbatuwa.

Akwai wani guri da ake cewa kwarin Gogau wato ita wannan babbar kwatar itace ta bi ta kwarin Gogau  in da unguwar Fagge take. Ko da mu ka kai ziyara wajen munga yadda ruwan ya yi gyara a wani layi da ake kira layin bola.

Kamar yadda wata mazauniyar unguwar da ambaliyar ta shafa Malama Lubabatu Fagge, ta shaida mana cewa ruwan gaba daya ya tafi da komai nasu, hatta abinci da ya ke ajiye a cikin gidajen su ruwa ya tafi da shi.

A unguwar ne mu ka ganewa idonmu wata dattijuwa da ruwan ya yi wa gyara a zaune a kofar gidan ta in da ta fito da ‘yan komatsenta ta shanya su.

Shi ma wani matashi da mu ka samu a unguwar mai suna Ibrahim ya bayyana mana yadda ruwan ya lalata musu shagon da suke kwana, inda yace yanzu dole ne ya koma dakin abokai ya yi maneji kafin su gyara, idan damina ta wuce.

Tabbas, abun da idanuwan mu su ka nuna mana akwai tausayi domin mutane da yawa sun rasa kayayyakin su. Koda muka duba magudanan ruwan unguwar Faggen hakika suma suna bukatar gyara da kulawa da ga ‘yan unguwar yadda ba sai gwamnati tazo ta yi ba.

Idan za’a iya tunawa dama hukumar nan mai kula da yanayi ta Najeriya ta bayar da hasashen samun ruwa mai yawa da ambiyarsa, tun kafin daminar ta kankama, to amma wata kil mutane ba su dauka abin zai kai haka ba.

A wani bangaren kuma, kwamishinan yada labarai na jihar Kano Mallam Muhammad Garba yace gwamnati ta kafa wani kwamiti mai karfi da zai bibiyi gine ginen da akayi akan magudanan ruwa inda yace duk ginin da aka gano baya bias ka’ida za’a rushe shi, kamar yadda ya shaidawa sashin Hausa na BBC.

Abin jira a gani shine, shin kwamitin da aka kafa don ya yi aikin binciken masababin ambaliyar; idan ya gabatar da rahoton sad a shawarwari za’a aiwatar dashi?

Domin ya zama al’ada, idan gwamnatoce sun kafa irin wadannan kwamituttuka, a karshe sai a jingine ko kuma ayi watsi da shawarwarin da aka bayar.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here