Hedkwatar Tsaron Najeriya tace bayanan ranar Lahadi da ke zargin cewa an kashe wasu fararen-hula da ba a bayyana adadinsu ba yayin hare-haen sama a Guradnayi, wani ƙauye kusa da Kusasu a Shiroro dake Jihar Neja ba ita ta kai wannan hari ba.
Hedkwatar tsaron Nijeriya ta musanta rahotannin da ke cewa fararen-hula sun mutu a wani harin sama da sojojin ƙasar suka kai a jihar Neja da ke arewacin ƙasar.
Hedkwatar tsaron ta ce sojojin sun kai hare-hare ta sama ne a wuraren da aka tabbatar cewa mafakar ‘yanbindiga ce a ƙaramar hukumar Shiroro ta jihar Neja.
Kafofin watsa labaran ƙasar sun ambato wata sanarwa da daraktan watsa labaran hedkwatar tsaron ƙasar, Manjo Janar Michael Onoja, ya fitar ranar Lahadi tana cewa an kai hare-haren ne bayan samun bayanan sirri da suka nuna haɗuwar ɓarayin daji a ƙauyen Lukupe na ƙaramar hukumar Shiroro ranar 9 ga watan Mayu na shekarar 2026.
Rundunar Sojin ta ce bayan wannan ne dakarun da ke aiki da jirage marasa matuƙa suka kai hare-haren sama tsakanin ƙarfe 11:59 na dare zuwa ƙarfe 6 na safiyar ranar 10 ga watan Mayu a maɓoyar ‘yanbindiga a ƙauyukan Katerma da Bokko Kusasu da Kuduru.
Manjo Janar Onoja ya bayyana cewa majiyoyin bayanan sirri na yankin sun tabbatar da cewa hare-haren sun “sauka a wuraren da aka nufa” a ƙauyukan Kusasu da Katerma da kuma Bokko.
Ya ce ce kimanin ɓarayin daji 70 aka kashe a Kusasu kaɗai, yayin da aka ga mayaƙan da suka tsira sun ɗauki gawarwakin abokansu domin binne su.
Sanarwar ta ce, “Bisa aikin da aka bai wa rundunar sojin Nijeriya na aikata ayyuka na kakkaɓe duk wani nau’i na rashin tsaro a ƙasar, ranar 9 ga watan Mayu na shekarar 2026, bayanan sirri sun nuna taruwar ‘yanbindiga a ƙauyen Lukupe na ƙaramar hukumar Shiroro.
”Daga baya, a ranar 10 ga watan Mayu na shekarar 2026 tsakanin ƙarfe 11:59 na dare zuwa ƙarfe 6 na safiya, rundunar jirage marasa matuƙa ta sojojin Nijeriya yayin da take aiki bisa bayanan sirri ta kai hare-hare na sama kan maɓoyar ‘yanbindiga a ƙauyukan Katerma da Bokko da Kusasu da kuma Kuduru a ƙaramar hukumar Shiroro ta jihar Neja.
“Ƙarin rahotanni daga majiyoyi daga yankin sun tabbatar da cewa hare-haren saman sun dira daidai kan wuraren da aka kai su a Kusasu da Katerma da kuma Bokko… An samu bayanan cewa kimanin ‘yanbindiga 70 ne hare-haren suka kashe a Kusasu. ”(TRT Hausa).





























