Home Noma da Kiwo Hybrid Da Sa’im Agrovet Sun Shirya Taron Karawa Masu Kiwun Kaji Illimi...

Hybrid Da Sa’im Agrovet Sun Shirya Taron Karawa Masu Kiwun Kaji Illimi A Kano

9
0
Kano Map 2

Daga: Suleiman Hussaini D/Kudu, Kano

Kamfanin samar da abincin kaji da sauran dabbobi na Hybrid Feed tare da hadin gwaiwar kamfanin dake dillancin kayan nasu Sa’im Agrovet sun shirya wani taro domin karawa masu kiwun kaji Illimi da sabbin dabarun kula da dabbobin nasu musamman a wannan lokaci da sanyi yake kawu kai.
Shugaban kamfanin na Hybrid Dr. Al-Amin Alhassan yace an Shirya taron ne da nufin ganawa da mikiyayan domin susan yadda kamfanin yake alfahari dasu tare da nuna musu wasu sabbin dabarun kiwun da Kuma yadda zasu ringa kare kayan su daga yanayin sanyi.
Ya Kuma kara da cewa mahalarta taron zasu samu cikakkan bayane akan wasu sabbin kayan abincin da kamfanin ya samar domin inganta sana’ar tasu. Inda yace kamfanin yana kukari sosai wajan bunkasa sana’ar abokan huldarsa.
Yayi bayanin cewa a lokacin taron kamfanin zai raba kyaututtuka ga wadanda sukafi yawun siyan kayan kamfanin da nufin kara musu kwarin gwaiwa tare da kara janyu wasu kustumomin, inda yace zasu bawa wanda yazu na daya kyautar mota wasu Kuma zasu sami kyautar firinji da sauran kyaututtuka.
Yayi Kira ga mahalarta taron dasu mai da hankali akan abubuwan da za’a koya musu a lokacin bitar, ya Kuma bada tabbacin cewa kamfanin zai ringa gudanar da irin wannan taron a duk shekara tare da bada wasu kyaututtukan.
Shima a nasa jawabin, wakilin kamfanin na Sa’im Agrovet Kuma mai kula da sashin kasuwancin na kamfanin Dr. Mujahid Sunusi Abdullahi yace makasudin shirya wannan bita ga masu sana’ar ta kiwun kijin shine domin su gana da musu sayar musu da kayan abincin da suke amfani dashi tare da basu shawarwari wadanda zasu taimaka musu domin bunkasa sana’ar tasu.
Ya Kuma nuna gamsuwarsa da ganin yadda mahalarta taron suka amsa gyayyatar da suke musu tare da Kira a garesu da cewa suyi amfani da irin abubuwan da aka kuyar dasu a wuraran sana’ar tasu domin samun irin ribar da suke bukata. Inda ya yabawa kamfanin na Hybrid bisa yadda yake samar da ingantaccen abincin dabbobi bama a iya kasar nan ba harma da wasu sassa na kasashen Afrika.
Da yake bayanin godiya a madadin sauran wadanda kamfanin yabawa kyautar kayan, Alhaji Shu’aibu Ibrahim wakilin gidan gonar Sabfarm dake garin Limawa wanda suka rabauta da kyautar mota, ya nuna farin ciki sa da wannan kyauta da suka samu. Inda yace hakan zai kara musu kwarin gwaiwa wajan kara sayan irin kayan da kamfanin yake samarwa.
Yace sun dade suna hulda da wannan kamfanin ba tare da samun wata matsala ba akan kayan da suke samarwa Kuma suna ganin amfanun kayan nasu duk da cewa suma suna samar da irin nasu kayan abincin amman hakan bai hana su sayan kayan kamfanin ba, wanda a cewar sa suna sayan abincin kaji Tirela daya a duk sati daga wajan su.
Ya Kuma bada tabbacin cewa zasu cigaba da amfani da irin kayan da kamfanin yake samarwa tare da cewar sune zasu sake lashe gasar da kamfanin zai sake bayarwar a shekara mai zuwa.
Mahalarta bita sun nuna jin dadin su tare da yabawa kamfanunowan bisa yadda suka shirya wannan bita, wanda a cewarsu zata taimaka musu wajan kara bunkasa sana’ar tasu.
Sun Kuma yi Kira ga gwamnati da sauran yan siyasa dasu ringa tallafawa wannan sana’ar tasu ganin irin amfanun da take dashi a cikin al’umma wanda a cewarsu hakan zai ringa taimaka musu wajan kara samar da abubuwan da ake bukata na kiji da sauran dabbobi.
Taron ya sami halartar yan Kungiyoyi manoma, masu sayar da kayan abincin kaji dama shuwagabannin kamfanonin da suke sarrafa kayan abincin.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here