Home Siyasa 2027: Hukumar INEC Ta Fitar Da Cikakkun Sunayen Yantakarar Gwamna A Nigeria

2027: Hukumar INEC Ta Fitar Da Cikakkun Sunayen Yantakarar Gwamna A Nigeria

15
0
2027 Yantakarar Gwamna

Ƴan Najeriya na ci gaba da tsokaci kan sunayen ƴantakarar gwamna da hukumar zaɓen ƙasar INEc ta fitar domin fafatawa a zaɓen 2027.

 

INEC ta tantance tare da amincewa da Kingsley Chinda a matsayin ɗan takarar gwamnan Jihar Rivers a zaɓen 2027, bayan ta saka sunansa cikin jerin ƴan takarar gwamnoni da ta fitar a daren Asabar.

 

Kingsley Ogundu Chinda tsohon jagoran yan adawa ne a Majalisar Wakilan Najeriya. sannan kuma tsohon mamba ne na jam’iyyar hamayya ta PDP.

 

Kingsley Chinda ya fara ɗaukar hankali watanni da suka gabata lokacin da ya zama ɗan takarar gwamnan Jihar Rivers na jam’iyyar All Progressives Congress (APC), alhali jama’a sun san shi a matsayin mamba na jam’iyyar PDP.

 

Daga nan ne ‘yan Najeriya suka fara tambayar lokacin da ya sauya sheƙa zuwa APC, da kuma ko har yanzu shi ne jagoran ƴan adawa a Majalisar Wakilai.

 

Bayan hukuncin da Kotun Ƙoli ta yanke a ranar 24 ga Satumba, 2026, sunan Kingsley Chinda ya sake ɗaukar hankali, sakamakon yadda hukuncin ya mayar da wasu tanade-tanaden Dokar Zaɓe ta 2026 da aka soke a baya.

 

Kotun Ƙolin ta yanke hukunci kan tanade-tanaden Dokar Zaɓen 2026 da suka shafi rijistar membobin jam’iyyun siyasa da kuma tsayar da ‘yan takara.

 

Kwamitin alƙalai bakwai da Mai Shari’a Adamu Jauro ya jagoranta ya soke hukuncin Kotun Ɗaukaka Ƙara da ya warware sashe na 77(5), 77(6), 77(7) da kuma 84(2) na dokar.

 

Waɗannan sassa na dokar sun shafi ƙa’idojin da suka danganci rijistar mambobin jam’iyyun siyasa, zaɓen fidda gwani kai tsaye, ko kuma tsarin maslaha wajen zaɓen yan takara da jam’iyyu ke amfani da shi.

 

Sakamakon wannan hukunci na Kotun Ƙoli, wata ƙungiya mai suna Association of Legislative Drafting and Advocacy Practitioners (ALDRAP) ta buƙaci Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta ta Ƙasa (INEC) ta hana Kingsley Chinda tsayawa takarar gwamnan Jihar Rivers a ƙarƙashin jam’iyyar APC a zaɓen 2027.

 

Ƙungiyar ta roƙi INEC da ta binciki “halaccin zaɓen fidda gwani na APC na takarar gwamna, sharuɗɗan da suka shafi rijistar mambobi, bayanan da APC ta miƙa wa INEC, da kuma matakan da suka dace domin aiwatar da hukuncin Kotun Ƙoli.”

 

Duk da wannan ce-ce-ku-cen, jam’iyyar APC a Jihar Rivers ta bayyana cewa “ba mu da wata matsala”, yayin da take mayar da martani kan sauya shekar ɗan takararta, Kingsley Chinda, zuwa jam’iyyar.

 

Da yake yanzu INEC ta fitar da jerin sunayen ƴan takara, hakan na nuna cewa babu wata matsala da ta hana shi tsayawa takara, kuma zai ci gaba da kasancewa ɗan takarar gwamnan Jihar Rivers na jam’iyyar APC a zaɓen shekarar 2027.

 

Jerin ƴantakarar gwamnan na kowace jiha

Abia

 

Opah Eric Chinemeucheya – APC

 

Kalu Kalu Agwu – ADC

 

Ijioma Uchechukwu Charles – APGA

 

Otti Alex Chioma – LP

 

Ogah Iroetugo Ndubuisi – NDC

 

Anosike Kelechi – PDP

 

Adamawa

 

Modibo Hammantukur Ribadu – ADC

 

Umaru Babangida Bajabure – ADP

 

Amini Ahmed Galadima – APC

 

Ishaku Elisha Cliff – LP

 

Dahiru Aishatu Ahmed – NDC

 

Vunobolki Maurice Michael – PDP

 

Akwa Ibom

 

John James Akpanudohedehe – ADC

 

Eno Umoh Bassey – APC

 

Jimmy Stella Monday – APGA

 

Mbaba Michael Bush – LP

 

Enyong Michael Okon – NDC

 

Brownson Ibanga Akpan – PDP

 

Bauchi

 

Halliru Dauda Jika -ADC

 

Shehu Jinda Yunusa – ADP

 

Abubakar Mohammed Abdullahi – APC

 

Aliyu Idris Muhammed – LP

 

Kashim Ibrahim Muhammed – NDC

 

Adamu Usman Ahmed – PDP

 

Benue

 

Hembe Iowase Herman – ADC

 

Nyimba Kwaghshir – ADP

 

Alia Hycinth Iormem – APC

 

Byuwan Mathias Terwase – LP

 

Shija Terhemba – NDC

 

Aondoakaa Michael Kaase – PDP

 

Borno

 

Babagana Buhari – ADC

 

Munguno Rufai Alhaji – ADP

 

Gubio Alhaji Mustapha – APC

 

Konto Umar – LP

 

Ibrahim Sanusi Kashim – NDC

 

Abba-Gana Ibrahim Baba – PDP

 

Cross

 

Otu Bassey Edet – APC

 

Obu Ogar Osim – LP

 

Archibong Arthur Javis – PDP

 

Joelyn Ita Hogan – Bassey – ADP

 

Delta

 

Ogboru Ovedje Great – ADC

 

Oborevwori Sheriff – APC

 

James Esther – LP

 

Itovwaye Chris – NDC

 

Mrakpor Peter – PDP

 

Obuseh Felix Ogechukwu – SDP

 

Ebonyi

 

Ukpai Mbah Udeh – ADC

 

Nwifuru Ogbonna Francis – APC

 

Nwodom Lucy Chinwe – APGA

 

Eze Oko Spledour – LP

 

Igwe Nwagu Palinus – NDC

 

Chukwuma Odii Ifeanyi – PDP

 

Enugu

 

Ocho Bodoeze Chukwuma – ADC

 

Mbah Peter Ndubuisi – APC

 

Ugwu Okwudilichukwu Chukwudera – LP

 

Ohaa Chiyeaka Christian – NDC

 

Nnaji Uchechukwu Geoffrey – PDP

 

Iloka Friday – SDP

 

Gombe

 

Bala Bello – ADC

 

Adeh Nuhu Milah – ADP

 

Gwamna Jamil Isyaku – APC

 

Muazu Zubairu Halilu – LP

 

Ardo Babayo Kumo – NDC

 

Jigawa

 

Sabo Mohammed Nakudu – ADC

 

Sulaiman Ibrahim – ADP

 

Namadi Umar – APC

 

Abdul’aziz Aminu – LP

 

Dutse Aminu Sani – NDC

 

Sule Mustapha Lamido – PDP

 

Kaduna

 

Sani Uba – APC

 

Isa Mohammed Ashiru – ADC

 

Bawa Shehu Usman – PDP

 

Abdulfattah Muhammad Aminu – PRP

 

Idris Adamu Abubakar – SDP

 

Rilwanu Muhammad Lawal -LP

 

Kano

 

Ibrahim Ali Amin – ADC

 

Muhammed Abdullahi – ADP

 

Yusuf Abba Kabir – APC

 

Santuraki Hamisu – LP

 

Abacha Muhammed Sani – PDP

 

Hussaini Bello Ado – SDP

 

Katsina

 

Ahmed Baba Kaita – ADC

 

Ahmed Murtala – ADP

 

Umar Dikko Radda – APC

 

Ilu-Barde Aliyu – NDC

 

Gard Yakubu Lardo – PDP

 

Kwara

 

Zakari Muhammed – ADC

 

Adeshina Ajisafe – ADP

 

Yakubu Danladi Salihu – APC

 

Abdulmunin Yinka Ajia – NDC

 

Kawu Suleman Bolakale – PDP

 

Amokanye David Adetoyese – NNPP

 

Kebbi

 

Malami Abubakar – ADC

 

Yahaya Ayuba – ADP

 

Idris Nasir – APC

 

Usman Aliyu – LP

 

Umar Faruk – SDP

 

Niger

 

Mohammed Kpataugi – ADC

 

Mohammed Umaru Bago – APC

 

Mohammed Adamu – APGA

 

Mohammed Usman – LP

 

Muhammed Yahaya Adam – NDC

 

Muhammed Mamman Nami – PDP

 

Lagos

 

Gbadebo Rhodes Vivour – ADC

 

Hamzat Kadri Obafemi – APC

 

Odunaike Oluwapemilerin Olurotimi – LP

 

Doherty Olufunsho Adeshina – NDC

 

Doherty Adedeji Olugbemiga – PDP

 

Olaniyi Olufemi – SDP

 

Ogun

 

Lawal Jimi Adebisi – ADC

 

Anifowose Johncrownfit Kayode – ADP

 

Adeola Solomon Olamilekan – APC

 

Ola Williams Adeyinka – SDP

 

Rivers

 

Pidomson Gabriel Baritulem – ADC

 

Kingsley Ogundu Chinda – APC

 

Boms Chima Ernest – LP

 

Lulu-Briggs Dumo Owukori – NDC

 

Ejekwu Samuel Soni – PDP

 

Ben-Gurion Peter – SDP

 

Nasarawa

 

Nuhu Angbazo- ADC

 

Christopher Mamman – ADP

 

Aliyu Ahmed Wadada – APC

 

Gaza Jonathan Gbefwi – LP

 

Emmanuel David Ombugado – PDP

 

Muhammed Abubakar Adamu – SDP

 

Oyo

 

Adegoke Taofeek Adeboyega – ADC

 

Alli Sharafadeen Abiodun – APC

 

Salami Gbolagade Tajudeen – APGA

 

Kareem Thompson Sola – LP

 

Yusuf Akim Adebola – NDC

 

Gbolarumi Hazeem Ola – PDP

 

Plateau

 

Sura John Sunday – ADC

 

Dawop Sani Sai’du – ADP

 

Muftwang Caleb Manasseh – APC

 

Nura Tanko – LP

 

Ropshik Kefas Wungak – PDP

 

Sokoto

 

Manir Muhammad Dan’iya – ADC

 

Sarkin Larabawa Nasiru – ADP

 

Aliyu Ahmed Sokoto – APC

 

Haliru Abubakar Dikko – LP

 

Aliyu Shamsudeen Ahmad – NDC

 

Abdullahi Sokoto Abubakar – PDP

 

Taraba

 

Abubakar Umar Tutare – ADC

 

Mamman Abubakar Mustapha – ADP

 

Kefas Agbu – APC

 

Shiddi Danjuma Usman – APGA

 

Nathan Sanda – LP

 

Yahaya Mohammed Sani – NDC

 

Bwacha Emmanuel – PDP

 

Yobe

 

Kassim Gaidam – ADC

 

Mohammed Nasiru Saleh – ADP

 

Wali Baba Mallam – APC

 

Kolomi Aji – LP

 

Ibrahim Mallam Shuaibu – NDC

 

Usman Abdullahi – PDP

 

Zamfara

 

Aliyu Bashir – APGA

 

Yusuf Sani – LP

 

Marafa Kabiru Garba – NDC

 

Shehu Gusau Ibrahim – PDP

 

Musa Hamza – SDP

(BBC Hausa).

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here