Home Ciyo Bashin N6.4Trn: Dalilin Mu Na Maka Gwamnoni A Kotu – SERAP

Ciyo Bashin N6.4Trn: Dalilin Mu Na Maka Gwamnoni A Kotu – SERAP

Ƙungiyar SERAP mai fafutukar yaƙi da cin hanci da rashawa a Najeriya, ta yi ƙarin haske akan dalilan kai ƙarar gwamnonin ƙasar 36 da kuma ministan birnin tarayyar Abuja gaban kotu.

Kungiyar ta ce ta shigar da wannan kara ne saboda rashin bayar da bayanai kan yadda gwamnonin jihohin Najeriya 36 da ministan Abuja, suka kashe kuɗaɗen da suka ciyo na bashin naira tiriliyan kusan shida, da kuma sama da dala billiyan 4 da rabi, ba tare da bahasi ba.(BBC).

SERAP ta buƙaci kotun da ta gayyaci hukumar EFCC da ICPC domin ƙaddamar da bincike kan yadda aka kashe basusukan da gwamnonin suka karɓo.

Kungiyar SERAP mai fafutukar yaƙi da cin hanci a Najeriya ta ce ta shigar da karar ne a ranar juma’ar makon da ya gabata a babbar kotun tarayya da ke Abuja.

NSERAP din ta ce, ta shigar da karar ne bayan gazawar gwamnonin wajen yi wa al’ummar su bayanin yadda suka kashe basusukan da suka karɓo da wajen da aka aiwatar da auikin da aka karbo bashin dominsu.

Kolawole Oluwadare mataimakin daraktan kungiyar ta SERAP ya yi karin bayani:

Ya ce: ’’Mun je kotu ne don a tursasa, tare da bai wa gwamnonin da ministan birnin Abuja umarnin bayar da bayani na yarjejeniyar da suka cimma da waɗanda suka basu bashin. Sannan mun buƙaci a gayyato hukumar yaƙi da cin hanci da rashawa ta EFCC, da hukumar yaƙi damasu yiwa tattali arzikin ƙasa ta’annati ta ICPC domin su ƙaddamar da bincike kan yadda aka ciw

o bashin. Yan Najeriya musamman na jihohin da aka ciwo bashin na da haƙƙin sanin yadda aka yi da kuɗaɗen, da yadda aka kashe su, da inda aka kashe su. Saboda haka bayyana irin waɗannan bayanai haƙƙi ne a kan masu mulki.’’

To kowa ne tasiri shigar da wanna kara zai yi? ganin cewar wannan bash ne karon farko ba da aka ji SERAP din ta shigar da karar kan batutuwa da dama, wanda wasu daga ciki har yanzu kotu bata kai ga fara saurararsu ba. Sai Kolawole Oluwadare ya yi karin bayani:

Clip;’’Waɗannan ƙararraki da SERAP ke shigarwa ba wai tana yi bane domin ƙashin kanta, tana yi ne don al’umma dogaro ga kundin mulkin Najeriya da ya bayar da yancin neman bayanai. Don haka, wannan jan ƙafa da ake gani na fara sauraron ƙararakin da muke shigarwa na da alaka da jan ƙafa da ake guskanta a ɓangaren shari’ar ƙasar. A ce sai an kai shekara uku da shigar da ƙara sannan za a fara sauraron ta, abu ne mai cike da damuwa.’’

Kolawole Oluwadare ya kuma jaddada cewa SERAP ba za ta taɓa yin ƙasa a gwiwa ba saboda irin waɗanan ƙalubale

Wanann dai na zuwa ne tun bayan da hukumar kula da basusuka ta Najeriya ta fitar da rahoton basusukan da ake bin jihohin kasar 36, da baban birnin ntarayayar kasar Abuja da ya kai naira tirliyan 5.9, da wanda siuka karbo a waje da ya kai dala biliyan 4.6.

Sai dai kawo yanzu ba a tsayar da ranar da zaa fara saurarar karar da SERAP din ta shigar ba. (BBC).