Antonio Guterres, Sakatare Janar na Majalisar Ɗinkin Duniya, ya ce ya zama dole duniya ta kalli yanayin zafin da ake ciki a matsayin wata matsala ta sauyin yanayi a duniya.
Hukumar kula da yanayi ta duniya ta ce ana buƙatar a yi shirye-shirye domin tunkarar tasirin yanayin inda ake da yaƙinin za a yi tsananin zafi a watanni masu zuwa.
Yanayin na iya janyo ɗumamar yanayi a sassan duniya.
Hakan na faruwa duk shekara biyu zuwa bakwai inda na ƙarshe ya janyo 2024 ta zama shekara mafi zafi a tarihi. (BBC Hausa).






























