Home Siyasa Ministoci: Dalilan Da Su Ka Sa Bamu Amince Da Elrufa’I Ba Da...

Ministoci: Dalilan Da Su Ka Sa Bamu Amince Da Elrufa’I Ba Da Sauran Mutum 2 – Sen. Buba

345
0
Sen. Buba 2

Majalisar Dattawa ta ce dalilan da suka sa ba su amincewa Shugaban Kasa, Bola Ahmad Tinubu ba da ya nada Tsohon Gwamnan Jihar Kaduna Nasiru Elrufa’i da sauran mutum 2  shine akwai akwai korafe-korafe akan su da kuma bincike da ake yi akan su ba a kammala ba.

Sanata Shehu Buba Umar da ke Wakiltar Bauchi ta Kudu ne ya sanarwa da Jaridar Viewfinder jimkada da kammala amincewa da Ministoci 45 da ga  cikin 48 inda, ya yi karin haske da cewa, “ ba wai ba za mu amince da sauran Ministocin guda 3 ba ne; abun da ya faru shine, akwai korafe-korafe akan su, sannan kuma ba’a kammala bincike akan su ba; amma da zarar an kammala zamu amince da su”

Sanata Buba ya kara da cewa akwai rubutattun korafe-korafe akan su kuma hakkin Majalisa ne ta bincika wadannan korafe-korafe; idan ta same su da laifi ko akasin haka zata rubutawa Shugaban Kasa shawara akan su don ya dauki matakin da ya dace.

Game da batum amincewa da Festu Kiyamo a matsayin Minista duk da cewa a lokacin tantancewa sun nu na basa goyon ba yan sa cewa; ai ya tuba kuma ya nuna nadama na abun da ya aikata a baya sabo da haka Majalisa ta sake bashi dama ko zai gyara kurakuren da ya yi a baya.

Akan batum Ministoci 45 da suka amince da su ya ce duk sun cancanta lura da irin bayanai da su ka gabatar a gaban Majalisar Dattawa kuma sun gamsu da irin bayanan da suka gabatar a gaban Majalisar shi ya sa suka amince da su.

Sanatan ya nuna irin jajircewa da suka yi wajen tantance Ministocin, inda suka shafe kwanaki 8 kuma su yi aiki tun da ga  safe har zuwa dare kuma sun yi tambayoyi masu ma’ana da zai tabbatarwa da Yan Najeriya ingancin Ministocin.

Sanatan ya kara da cewa duk da korofi da ake yi kan Ministocin cewa sun yi yawa, yace yawan na su ba illa bane duk da kamfar kudi da ake das hi a kasarnan;  ya ce nadin nasu ya bayar da damar samun wakilci a bangarori da dama a jihohi.

Ya bayar da misali da Jiharsa ta Bauchi wanda suke da Ministoci guda 2 inda ya ce da shi da sauran Yan uwansa Yan Majalisar Dattawa dag a Jihars sun bayar da wakilci a bangarori da ke jihar wanda kowanne bangare ya sa mu wakilci.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here