Home Diplomasiyya Yakin Iran: Majalisar Wakilan Amurka Ta Umarci Trump Daya Janye Dakarun Kasar

Yakin Iran: Majalisar Wakilan Amurka Ta Umarci Trump Daya Janye Dakarun Kasar

1
0
Trump

An umarci Shugaba Kasar Amurka, Donald Trump da ya janye sojojin Amurka daga yakin Iran, ko kuma ya nemi amincewar majalisun dokokin ƙasar kan ci gaba da yaƙin.

 

Majalisar wakilai ta Amurka ce ta bayar da umarni bayan da ta kaɗa ƙuri’a inda ta umarci, Shugaban daya janye dakarun kasar daga yakin.

 

Ƴan majalisar daga jam’iyyar Republican huɗu sun goyi bayan ƴan Democrats wajen amincewa da wannan mataki wanda yanzu zai wuce zuwa majalisar dattawan ƙasar.

 

Matakin da aka ɗauka dai ya kasance na je-ka na yi-ka ne a yayin da shugaban ƙasa ke da ikon hawa kujerar na-ƙi a kan duk wani hukunci ko matakin da ya ga zai ka wo masa matsala a shugabancinsa.

 

Wannan shi ne matakin na baya-bayan nan na kara nuna adawa da matakin Trump din a kan Iran, daga cikin jam’iyyarsa ta Republican.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here