Hukumar kula da wutar lantarki a Najeriya NERC ta fara amfani da wani tsari wanda zai bai wa masu amfani da sola damar siyar wa hukumomi lantarki.
NERC ta bayyana haka ne a shafinta na X inda ta ce “idan sola ɗinku na samar da lantarki fiye da buƙatarku, za ku iya sayar wa kamfanonin rarraba lantarki ƙarin wuta kuma a biya ku kuɗi”
A cewar NERC, wannan tsarin shi ake kira Prosumer a Turancin Ingilishi wato inda kwastoma zai kasance mai amfani da kuma samar da lantarki.
Sai dai akwai ƙa’idoji da ke tattare da tsarin da suka haɗa da dole ka zama kwastoma a kamfanin rarraba lantarki sannan kuma dole sola ɗin da mutum ya saka ta zama mai ƙarfin 50kwp.
Kazalika, dole sai mutum ya samu izini daga kamfanin rarraba lantarki bugu da ƙari kuma sai ka sa hannu kan yarjejeniya ta sabon tsarin sannan kuma mutum sai ya yi rajista da NERC.
Sanarwar ta ce tsarin bai shafi gidaje masu amfani da matsakaicin sola ba.






























