Home Wasanni Maroko ta baiwa magoya bayanta tikiti dubu 13 domin kallon wasanta da...

Maroko ta baiwa magoya bayanta tikiti dubu 13 domin kallon wasanta da Faransa

334
0

Hukumar da ke kula da kwallon Maroko ta siya wa magoya bayanta tikiti dubu goma sha uku kyauta domin kallon wasansu da Faransa a gasar cin kofin duniya da ke gudana a Qatar.

A gobe Laraba za a buga wasan kusa da karshe a tsakanin kasashen biyu bayan Maroko ta kafa tarihi a matsayin kasar Afrika ta farko da ta kai wannan matakin.

Haka kuma kamfanin jirgin sama na kasar watau Royal Air Maroc ya saka jirage 30 a farashin mai rahusa ga ‘yan kallo domin su yi balaguro zuwa Qatar.

An yi shagulgula sosai a Maroko tun bayan da kasar ta samu galaba a kan manyan kasashen Turai a gasar da Qatar ke daukar bakunci.

A daya wasan kusa da kashe Argentina ce za ta kara da Croatia a yau Talata.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here