Home Siyasa ‘Buri Na Shine Na Tallafawa Marasa Karfi Mutum 1.5m A Karamar Hukumar...

‘Buri Na Shine Na Tallafawa Marasa Karfi Mutum 1.5m A Karamar Hukumar Katsina’ – Inji Hon. Chindo

195
0
Hon. Chindo 2

Hon. Aminu Chindo Dan Majalisar Wakilai dake Wakiltar Karamar Hukumar Katsina ya ce zai ci gaba ta tallafawa matasa da masu karamin karfi a Karamar Hukumar Katsaina. Inda ya ce burinsa shine ya tallafawa sama da mutum miliyan daya da dubu dari biyar(1.5m) a cikin shekaru hudu masu zuwa.

Shugaban Kwamitin Tsaron na Cikin gida na Majalisar Wakilai,Hon. Aminu Chindo, ya sanar da haka ne a hirarsa ta yan jaridu a ofishinsa dake Abuja a ranar Talata.

Ya ce hakan ya biyo bayan rashin aikin yi da ya addabi matasa a Karamar Hukumar Katsiana ya ce shirye shirye sunyi nisa wajen ganin ya samar da aiyukanyi ga matasa a Karamar Hukumar dama Jihar Katsina baki daya.

Dan Majalisar ya ce Majalisar Wakilai ta sha alwashin ganin ta tallafawa Jihar Katsina wajen ganin an sami ingantaccen tsaro a jihar Katsina dama Najeriya baki daya domin samar da zaman lafiya da kwanciyar hankali da wanzuwar arziki a kasarnan.

Ya ce babban burinsa shine ya ga an sami ingantaccen tsaro a jihar Katsaina da Arewa maso Yamma dama Najeriya baki tare da samar da aikin yi ga matasa domin sune kashin bayan cigaban al’umma.

Hon. Chindo 1

Hon. Chindo ya kara da cewa Jihar Katsina na fama da kalubale na tsaro sabo da haka zaiyi dukkan mai yiwu na ganin an samar da mafita ta hanyar yin amfani da dukkan hanyoyin da suka kamata wajen ganin an sami ingantaccen tsaro a jihar.

Dan Majalisar ya ce, suna fama da matsalar yan gudun hijira a jihar a sakamakon barazanar tsaro wanda ya haifar kuncin rayuwa ga dubbun mutane. Ya kara da cewa, hakan ya haifar da hana manoma zuwa gona da kasuwanci a Jihar Katsina da Arewa maso Yamma.

Ya yabawa Gwamnan Jihar Katsina, Dikko Radda ganin yadda yake fadi tashi wajen ganin an sami ingantaccen tsaro a Jihar Katsina; inda ya ce zasu hada karfi da karfe wajen ganin an sami kyakkyawan tsaro a Jihar.

Hon. Chindo ya ce tuni sun fara tattawa da hukumomin tsaro kamar su Civil Defense dama masu samar da tsaro na sakai wajen ganin an maganta matsalar tsaro da ta addabi Jihar.

Daga karshe, ya yi kira ga mutanen Karamar Hukumar Katsina dana Jihar Katsina dama Arewa maso Yamma da su basu hadin kai da goyon baya wajen ganin an sami ingantacce tsaro da zaman lafiya a yankin baki daya.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here