Home Ilimi Kungiyoyin Fulani Makiyaya Sun Nemi Majalisar Wakilai Da Kada Ta Bari A...

Kungiyoyin Fulani Makiyaya Sun Nemi Majalisar Wakilai Da Kada Ta Bari A Hada Hukumar Ilimin Makiyaya Da Wata Hukuma

154
0
Hon. Almustapha A 2

Gamayyar Kungiyoyin Makiya sun roki Majalisar Taraiya da ta taimaka wajen ganin ba a hade Hukumar Ilimin Makiya ta Kasa da wata Hukuma ba ganin cewa yin haka zai kawo cibaya wajen yunkurin da a ke yi  na ganin an samawa Fulani makiya ilimin zamani mai inganci a Kasarnan.

 

Kungiyoyin sun yi wannan kira ne a ranar Alhamis a yayin da su ka baiyana a gaban Kwamitin Majalisar Wakilai na Ilimi na Musamman domin gabatar masa da bukatar su na ganin hadakar bata tabbata ba.

 

Mataimakin Sakatare na Kungiyar Miyetti Allah ta Kasa, Yahaya Isa ya yiwa Yan Jaridu Karin haske na baiyanar su a gaban Kwamitin in da ya ce sun lura cewa akwa yunkuri na hade Hukumar Makiyaya ta Kasa da Hukumar Ilimin Manya da ga Gwamnatin Taraiya.

 

Ya ce hade wadannan Hukumomi guri guda zai haifar da babbar matsala  da zata kawo nakasu a yunkurin da ake yin a samar da ilimi zamani mai inganci ga makiyaya musamman a wannan lokaci da barazanar Tsaro ta yi tsamari musamman a  Arewacin Kasarnan.

 

Isa ya kara da cewa a halin yanzu Hukumar Makiyaya ta Kasa ta na da sama da Makarantu dubu bakwai da Malamai sama da dubu biyu da dalibai sama da yara miliyan biyu da su ke karatu a  mataki daban-daban a kasarnan. In da ya kara da cewar manufar da ta sa aka kafa wannan Hukuma ya sha ban-ban da manufar da aka kafa Hukumar Ilimin Manya.

 

Sabo da haka ya ce hada su zai haifar da Karin matsalar da ake fuskanta ta rashin isassun kudade da malamai da kayan aiki da sauran bukatu da ake da su a Hukumar.

 

Isa ya kara da cewa matsaloli na tsaro da ake fama da su a Kasarnan su na da alake ne da jahilci musamman na rashin ilimin addini da na zama ga Makiyaya. In da ya ce yanzu ne lokacin da ya dace Gwamnatin Taraiya ta kara kaimi na bayar da wadatattun kudade da kayan aiki ta yadda za a yaki jahilci wanda shi ne ummul aba’isun barazanar Tsaro da ake fuskanta a Kasarnan.

 

Ya ce wannan Tsari na Ilimantar da Makiyaya da akeyi na tsawon shekaru 25 da su ka gabata ya haifar da masu ilimi da ga masu Digiri na daya da na biyu kai harma da farfesa, wanda ya ce idan aka inganta harkar zai taimaka wajen samar da likitoci da injiniyoyi da kwararru a fannoni daban- daban.

 

A yayin gabatar da nasa jawabin a gaban Kwamitin daya da ga cikin Daraktocin Hukumar ta Ilimin Makiya ya tabbatar da bayanai da Yan Kungiyar Miyetti Allah da MACBAN su ka gabatar in da ya ce hukumar a shirye take ta gabatar da dukkannin bayanai da su ke nuna irin kokarin da Hukumar ta yi da wadanda ta ke so ta yi a gaban Kwamitin na Majalisar Wakilai.

 

Daraktan ya bukaci Majalisar Wakiai da ta tallafawa Yunkurin Hukumar na sama mata da wadatattun kudade da za su tallafawa yunkurin Hukumar na aiwatar da aikace-aikace da Doka ta tanadarwa Hukumar.

 

A na sa jawabin Shugaban Kwamitin Ilimi na Musamman na Majalisar Wakilai, Hon. Ibrahim Almustapha ya yabawa kokarin shugabannin Hukumar da Kungiyoyin Miyetti Allah da MACBAN da sauran su da su ke ta fadi tashi wajen ganin Makiyaya sun sami ilimi mai inganci.

 

In da y a ce Majalisar Wakilai za ta yi duk mai yiwuwa wajen ganin Hukumar ta Kula da Ilimin Makiyaya ta samu kulawar da ta kamata sai dai ya ja hankalin su da su samar da bayanai da za su gamsar da Gwamnati cewa zaman Hukumar na cin gashin kanta yafi a hada ta da wata Hukumar.

 

Har ila yau. Ya ja hankalin Hukumar na bukatar su ilimantar da Yan Najeriya na irin aikace –aikace da Hukumar ta ke yi domin su gamsu cewa eeh lallai ya cancanta a bawa Hukumar yancin cin gashin kanta.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here